Hukumar 'yan sandan Najeriya ta yi wa manyan jami'ai 507 karin girma

Hukumar 'yan sandan Najeriya ta yi wa manyan jami'ai 507 karin girma

A wata sanarwa da jaridar The Nation ta ruwaito, hukumar 'yan sandan Najeriya ta bayar da lamuni akan yi wa wasu manyan 'yan sanda shida nadin mukamin mataimakin sufeton 'yan sanda wato matsayin DIG, a yayin da biyu cikin su za su tafi hutun ajiye aiki.

A sanarwar da kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya, Ikechukwu Ani ya fitar a birnin Abuja, sabbin mataimakan sufeton 'yan sandan hudu za su maye gurbin hudun da suka yi ritaya daga aiki kuma za su kasance cikin tawagar babban sufeton 'yan sandan Najeriya da ta kunshi mataimakan sufeton 'yan sanda bakwai.

Sanarwar ta bayyana sunayen sabbin mataimakan sufeton 'yan sandan da suka samu karin girma zuwa matsayin DIG kamar haka; Abdul Dahiru Danwawu; Lawal Shehu; Adeyemi Samuel Ogunjemilusi; Peter Babatunde Ogunyanwo, Alex Okpara da kuma Celestine Okoye. Ogunjemilusi da kuma Okpara su ne wadanda za su tafi hutun ritaya daga aiki.

Hukumar ta kuma amince da karin girman kwamishinonin 'yan sanda 14 zuwa matsayi na gaba wato AIG. Sun kasance; Yunana Babas; Dan-Malam Mohammed; Mua’zu Zubairu Halilu; Rabiu Yusuf; Sanusi Nma Lemu; Ahmed Iliyasu; Mohammed Uba Kura; Zaki M. Ahmed; da Gwandu Haliru Abubakar.

Sauran sun hadar da; Bashir Makama; Zama Bala Senchi, kwamishinan 'yan sandan jihar Jigawa; Bello A. Sadiq; Austin Iwero Agbonlahor; Lawan Ado, tsohon kwamishinan 'yan sandan jihar Kwara kuma Kwamandan makarantar koyon aikin dan sanda da ke jihar Kaduna.

Hukumar 'yan sandan Najeriya ta bayar da lamunin wannan karin girma yayin taronta na shida da ta gudanar bisa jagorancin Musiliu Smith, cikin birnin Abuja tun a ranar Juma'a, 18 ga watan Oktoba.

KARANTA KUMA: Trudeau ya sake lashe zaben shugabancin kasar Canada

Hukumar ta kuma aminci da karin girman manyan jami'a 230 da ke mukamin SP zuwa CSP, DSP 11 zuwa mukamin SP da kuma ASP 211 zuwa mukamin DSP. Sai kuma jami'ai 41 daga mukamin Inspector zuwa ASP1.

Sabbin manyan sufurtandojin wato CSP sun hadar da; Kabiru Ishaq; Sufi Salisu Abdullahi; Dattijo Abdullahi; Bisiriyu Akindele; Faloye Folusho; Ngozi Faith Nwosu; Shehudden Yusuf Baba; Ibrahim Bashir; Benjamin Nlemchukwu Ugwuegbulam; Remigius Nnaemeka Ekpe; Tope Adewunmi Oparinde; Esther Ifeoma Nwaiwu, Victoria Olayinka Mulero da Ogbonnaya Nwota.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel