Kwankwaso zai kara daukar nauyin yaran talakawa zuwa kasashen turai domin karo ilimi a jihar Katsina

Kwankwaso zai kara daukar nauyin yaran talakawa zuwa kasashen turai domin karo ilimi a jihar Katsina

- Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta dauki kudurin taimakawa yaran talakawa marasa galihu a jihar Katsina domin ba su ingantaccen ilimi

- Yanzu haka dai ana ta faman shirye-shirye akan wannan sabon tsari da tsohon gwamnan Kanon ya kai jihar ta Katsina

- Idan ba a manta ba watannin da suka gabata ne Kwankwaso ya dauki nauyin kimanin dalibai 250 zuwa kasar Indiya da Sudan domin karo ilimi

Yanzu haka dai gidauniyar Kwankwasiyya tana ta faman shirye-shirye a jihar Katsina domin daukar nauyin 'ya'yan talakawa marasa galihu wajen ba su ingantaccen ilimi.

Gidauniyar ta dauki wannan kuduri ne domin ganin ta ingantan ilimin yaran talakawan domin samun cigaba a rayuwar su.

Da aka yi hira da shugaban wata kungiyar mai suna 'Pleasant Library and Book Club (PLBC)', Engr. Muttaqha Rabe Darma, ya ce ya gayyaci gidauniyar ta Kwankwasiyyar ne zuwa jihar Katsina domin tayi irin abinda tayi a jihar Kano, domin taimakawa yaran talakawa marasa galihu su samu ingantaccen ilimi.

"Na taba jin tsohon gwamnan jihar Kano Eng. Rabiu Musa Kwankwaso yana cewa zai bada irin wannan tallafin da yake bawa yaran talakawa a jihar Kano ga sauran jihohin yankin arewa, hakan yasa na gayyato su domin ayi a jihar Katsina.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya na bawa 'yan Najeriya marasa karfi 621,000 naira dubu biyar a kowanne wata - Maryam Uwais

"Na tabbata da irin kokarin da Kwankwaso yake yi na ganin ya kawo cigaba a jihohin mu na arewa, 'ya'yan talakawa za su more," in ji shi.

Engr. Muttaqha kuma ya kara da cewa shima ya taba yin abu makamancin haka inda ya dauki nauyin sama da yara 140 domin inganta iliminsu da kudin shi a lokacin da yake shugaban PTDF.

Idan ba a manta ba kimanin mutane 250 ne Kwankwaso ya dauki nauyin su domin zuwa su karo ilimi a kasasr Indiya da Sudan, wanda gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta dauki nauyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel