Wani mutum ya mutu yana sassarfa a Legas

Wani mutum ya mutu yana sassarfa a Legas

Wani mummunan bala'i ya auku a birnin Ikko na jihar Legas yayin da ajali ya katse hanzarin wani mutum yana tsaka da sassarfa a kan hanyar WEMCO da ke yankin Ogba da sanyin safiyar ranar Lahadin da ta gabata.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, mutum wanda ba'a bayyana sunansa ba ya yanke jiki ya mutu a sanadiyar bugun zuciya da aka yi ta kokarin ceto rayuwarsa amma nan take ya ce ga garinku nan.

A wani faifan bidiyo da manema labarai suka samu damar lekawa cikinsa, sun hangi gawar matashin a kan titi ruwan sama na sauka a kanta sanye da rigar kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da kuma fararen takalma sau-ciki.

Wani mutum da abin ya faru a kan idonsa, Ayobami Adedeji, ya shaidawa manema labarai cewa, mutum bayan ya yanke ya fadi ya kuma rinka numfashi da kyar da har sai da ya cika gabanin a gayyato kwararrun kiwon lafiya suka kawo masa dauki.

Da dama an yi ikirarin cewa, duk da dai ajali da ya yi kira sai an amsa, akwai yiwuwar ana iya ceto rayuwar matashin da cutar bugun zuciya ta riska ba tare da aune ba.

A wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, bala’i ya auku akan al'ummar kauyen Amasiri da ke cikin karamar hukumar Afikpo ta Arewa a jihar Ebonyi, inda wani Ango mai suna Mista Chukwuemeka Onwuka ya yanke jiki ya fadi a wajen shagalin bikinsa.

KARANTA KUMA: Gobara ta kona shaguna 300 a kasuwar Benin

Kamar yadda Jaridar Punch ta rahoto, Chukwuemeka Onwuka ya kife ne a lokacin da ake cikin shagalin bikin aurensa da Onyinyechi Amadi Ugbor, da ta kasance amaryarsa.

Kamar yadda wadanda abin ya faru a gabansu su ka bayar da shaida, sun ce wannan Ango bayan ya tiki rawa tare da ‘yan uwa da abokan arziki a wurin shagalin da aka shirya domin murnar daurin aurensa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel