Almajirina ne ya jagorancin masu garkuwa da mutanen da suka sace ni - Babban Malamin Islama

Almajirina ne ya jagorancin masu garkuwa da mutanen da suka sace ni - Babban Malamin Islama

Alhaji Jamiu Zakariyahu, Malamin addinin Islama ne da aka sace tare da yin garkuwa da shi a ranar 2 ga watan Oktoba, 2019, a garin Ajowa Akoko da ke karkashin karamar hukumar Akoko ta arewa maso yamma a jihar Ondo.

A yayin wata hirarsa da jaridar Punch, Jamiu ya bayyana yadda aka sace shi da kuma wadanda keda hannu a ciki lamarin.

"Na kasance limami a wani masallaci da ke unguwar Daja a garin Ajowa Akoko. A ranar 2 ga watan Oktoba wasu mutane suka sace ni a hanyata ta koma wa gida bayan sallar Isha.

" Ina cikin tafiya a kan Babur dina sai kawai wasu mutane, su biyar, suka haske min ido da cocilan a yayin da ya rage taki kadan na karasa gidana.

"Na rikice saboda haske min idon da suka yi, nan da nan sai na taka birki, kafin na ce uffan sun saka min hular sanyi, sun rufe min fuska, sannan suka tafi da ni," a cewar Jamiu.

Malam Jamiu ya bayyana cewa sai bayan da aka kama wadanda suka yi garkuwa da shine sannan ya fahimci cewa akwai wani tsohon almajirinsa mai suna Wasiu Mohammed, wanda ya koyar a makarantar Islamiyya.

DUBA WANNAN: Hassan da Usaini: Alakar da ke tsakanin Buhari da Mamman Daura duk da banbancin shekaru biyar da ke tsakaninsu

"Har na gama zama na a hannunsu basu bude min ido ba, kuma basu bari na yi Sallah koda sau daya ba.

" Suna samun labarin duk abinda ke faruwa a gari, don duk ziyarar da jami'an tsaro suka kai gida na, sai da suka sanar da ni tare da yi min barazanar cewa babu wanda ya isa ya kubutar da ni daga hannunsu," kamar yadda Jamiu ya bayyana.

Malamin addinin ya kara da cewa wadanda suka sace shi 'yan kabilar Yoruba ne tare da bayyana cewa sun iya turanci sosai, wata alama da ke nuna cewa sun yi karatu mai zurfi.

Malam Jamiu ya shawarci gwamnati ta samar da guraben aiyuka ga matasa domin a samu zaman lafiya da raguwar aikata miyagun laifuka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel