Kano: Kwararru sun yi amfani da dabarar kimiyya wajen kama Zakin da ya kwace a gidan 'Zoo'

Kano: Kwararru sun yi amfani da dabarar kimiyya wajen kama Zakin da ya kwace a gidan 'Zoo'

Babban manajan darektan gidan adana namun daji na (Zoological Farden) Kano, Alhaji Usman Gwadabe, ya tabbatar da cewa kwararru sun samu nasarar kama Zakin da ya fice daga wurin ajiyarsa da yammacin ranar Asabar.

Gwadabe ya ce kwararrun sun yi amfani da hikimar kimiyya ta sa dabbobi masu hatsari bacci kafiin su samu nasarar kama Zakin da safiyar ranar Lahadi.

Shugaban ya shaida wa manema labarai a garin Kano cewa kwararrun sun samu nasarar kama Zakin tare da hadin gwuiwar jami'an 'yan sanda da sauran jami'an tsaro.

Ya kara da cewa kwararrun da jami'an tsaron na kokarin ganin sun mayar da Zakin zuwa cikin kejnsa da ke gidan 'Zoo' din.

A daren ranar Asabar ne, Legit.ng ta wallafa labarin cewa tashin hankali da tsoro sun samu mutanen tsakiyar birnin Kano a daren ranar Asabar, 19 ga watan Oktoba 2019 bayan Zaki ya kwace daga hannun masu kula dashi a gidan Zoo din Kano.

Wata majiya ta sanar da jaridar Daily Nigerian cewa, Zakin ya kubce ne bayan da aka fita da shi wani shirin noma da kiwo a yammacin ranar Asabar.

DUBA WANNAN: Hassan da Usaini: Alakar da ke tsakanin Buhari da Mamman Daura duk da banbancin shekaru biyar da ke tsakaninsu

Masu kula da shi sun yi kokarin mayar da shi amma ya rinjayesu tare da fin karfinsu.

Duk da cewa, hukumar gidan zoo din bata ce komai akan aukuwar hakan ba, amma mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Kiyawa ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Amma ya ce, har yanzu Zakin yana nan titin gidan Zoo din duk da ba a san inda yake ba. Ya kara da cewa, an tura runduna don nemo Zakin tare da 'yan sandan da zasu kwantar da hankulan jama'ar yankin.

Kiyawa ya ce, ba a samu rahoton cewa Zakin ya raunata wani ko ya illata koda dabba ba har yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng