Bidiyo: Ta tabbata ya koma fim, an nuno sabon fim din da Sanata Dino Melaye ya fito a ciki
- Ashe dai da gaske ne cewa tsohon Sanatan jihar Kogi ta yamma Dino Melaye ya koma harkar fim
- Domin kuwa a karon farko an hasko shi a cikin wani sabon fim mai suna 'The Crescent' wanda kamfanin shirya fina-finai na kudancin Najeriya ya shirya
- Idan ba a manta ba Sanatan dai ya rasa kujerar shi a makonnin da suka gabata bayan kotu ta tsige shi
Kowa dai ya san cewa Sanata mai wakiltar jihar Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye dan dirama ne, yanzu haka dai Sanatan yana nuno kwarewar shi a harkar fim, bayan an nuno shi a wani sabon fim da ya fita na kamfanin fina-finai na Kudancin Najeriya Nollywood.
Yanzu haka dai ana kokarin sanyawa Sanata Dino Melaye suna ne na 'yan fim, saboda ana ganin cewa wannan ita ce hanya ta farko da zai iya dacewa ya samu shiga zuwa makarantar koyar da harkar fim ta kasar Amurka mai suna 'Hollywood Film Academy'.
KU KARANTA: Wani mutumi ya turawa babban amininshi 'yan daba su kashe shi, bayan ya ari naira dubu dari biyu ya kasa biyan shi
Sanatan dai an nuno shi a jikin fastar wani sabon fim da ya fito na Nollywood mai suna 'The Crescent', inda aka nuno hoton shi dana fitaccen jarumin nan na Kannywood Yakubu Mohammed da kuma wasu daga cikin jarumai na Kudancin Najeriya.
Idan ba a manta ba a makonnin da suka gabata ne wata kotu ta tsige Sanatan daga kujerar shi, inda ta bayyana cewa sai an sake gabatar da zabe. Wannan lamari dai ya zo ne jim kadan bayan Sanatan ya sha kasa a zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP, bayan ya fito neman takarar gwamnan jihar ta Kogi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng