Innaillahi wa’inna illahi raji’un: Bam ya halaka mutane 62 a masallacin Juma’a a Afghanistan

Innaillahi wa’inna illahi raji’un: Bam ya halaka mutane 62 a masallacin Juma’a a Afghanistan

- Akalla masallata 62 ne suka rasa ransu sakamakon wani harin bam da aka kaddamar ana tsaka da sallar Juma'a, a Afghanistan

- An kuma tattao cewa wasu da dama sun jikkata a harin, inda karfin tashin bam din ya yaye rufin gidaje da dama

- Masallacin da aka kai harin ya kasance a gundumar Haska Mina, kilomita 50 daga birnin Jalalabad

Rahotanni sun kawo cewa akalla mutane 62 ne suka rasa ransu sannan da dama suka jikkata sakamakon wani harin bam da aka kaddamar ana tsaka da sallar Juma'a, a Afghanistan.

Shafin BBC ta rahoto daga wani shaida da lamarin ya afku a idonsa cewa karfin tashin bam din ya yaye rufin gidaje da dama.

Sai dai zuwa yan an tattaro cewa babu wani wanda ya dauki alhakin kaddamar da harin.

Harin na zuwa ne bayan rahoton Majalisar Dinkin Duniya na cewa adadin fararen hular da suka mutu a kasar ta Afghanista ya zarce tunani.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, an kashe yan farar hula 1,174 tsakanin watannin Yuli da Satumba.

KU KARANTA KUMA: An gurfanar da wani dan shekara 60 bayan ya yaudari wata bazawara da alkawarin aure

Attaullah Khogyani, mai magana da gwamnan lardin ya bayyana cewa mutane 62 aka kashe sannan mutum 36 sun samu raunuka a harin da aka kai wa masallata.

Masallacin da aka kai harin ya kasance a gundumar Haska Mina, kilomita 50 daga birnin Jalalabad.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel