Hotunan Bella Hadid: Mace Musulma da tafi kowacce mace kyau a duniya
- Bella Hadid Musulma ce 'yar kasar Amurka, an bayyana ta a matsayin macen da tafi kowacce mace kyau a duniya
- Daga ita kuma sai fitacciyar mawakiyar nan 'yar kasar Amurka wato Beyonce ita ce ta zo ta biyu a cikin jerin matan
- Haka kuma mawakiya Ariana Grande da kuma Taylor Swift sune suka zo ta hudu da ta biyar a cikin jerin matan
Tauraruwar tallar kaya, wacce take Musulma 'yar kasar Amurka mai suna Bella Hadid ita ce aka bayyana a matsayin macen da tafi kowacce mace kyau a duniya.
An yi amfani da wata manhaja ta lissafi na kimiyya ta mutanen kasar Girka dake bayyana kyan fuska wanda ake kira da 'Golden Ratio of Beauty phi' a turance, wannan abin lissafi dai ya bawa Bella Hadid maki 94.35.
Sai dai kawai an bayyana wata matsala guda daya da Bella ta samu shine girman goshinta.
Wacce ta zo ta biyu a wajen kyau, ma'ana mai biyewa Bella Hadid ita ce mashahuriyar mawakiyar nan ta kasar Amurka wato Beyonce, wacce ita kuma ta samu makin kyawun fuska da wannan abu na lissafi yayi ya bata maki 92.44.
KU KARANTA: Babbar magana: Duk muna daura guru da laya a jikinmu, kuma muna zuwa wajen bokaye - In ji wani dan majalisa
Sai kuma mace ta uku ita ce jarumar fim sannan kuma mai tallar kayan sawa, Amber Heard wacce ta samu maki 91.85.
Sai kuma ta hudu shahararriyar mawakiyar nan mai suna Ariana Grande ta samu amki 91.85. Haka kuma mawakiya Taylor Swift ta zo ta biyar a cikin jerin matan inda ta samu maki 91.64.
Likitan gyaran fuska na kasar Ingila, Dr Julian De Silva shine ya fitar da wannan kiyasi kamar yadda jaridar The Mail ta ruwaito.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng