Buhari ya yi umurnin binciken hukumar raya Niger Delta, ya ce bai san inda dukka kudaden suka shiga ba

Buhari ya yi umurnin binciken hukumar raya Niger Delta, ya ce bai san inda dukka kudaden suka shiga ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin kaddamar da binciken kwakwafi kan ayyukan hukumar raya yankin Neja Delta mai arzikin man fetur.

Buhari ya yi umurnin bincikar hukumar tun daga shekarar 2001 har zuwa bana, a lokacin da ya karbi bakuncin gwamnonin jihohin yankin a ranar Alhamis, 17 ga watan ktoba.

Kakakin Shugaban kasar, Mallam Garba Shehu, ya ce za a binciki hukumar ne tun daga kafa ta tsawon shekaru takwas sakamakon krafe-korafen da suka yi yawa game da ayyukanta.

A cewarsa, Shugaban kasar ya kosa da korafe-korafen da suka da ake yi akan hukumar wajen gazawarta na gudanar da ayyukanta da kuma yadda ake tafiyar da harakar kudaden na al'umma.

Ya kara da cewa Buhari yana son a gano inda kudaden hukumar ke shiga, bayan shekara biyu zuwa uku an kara yawan kudaden da ake ware wa hukumar a kasafin kudi.

KU KARANTA KUMA: Mafi karancin albashi: Gwamnatin Katsina za ta zauna da NLC domin fitar da tsari na musamman

Sai dai bai yi karin bayani ba game da kwamitin da zai gudanar da binciken da kuma lokacin da zai soma aiki.

An ambato Buhari na cewa abin da ake gani yanzu haka a yankin Kudu maso kudu, bai yi daidai da tarin dukiyar da aka rika warewa wannan hukuma ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel