Babbar magana: Babu ni ba talaka a rayuwata, hanyar sa daban tawa daban - Jaruma Nikki

Babbar magana: Babu ni ba talaka a rayuwata, hanyar sa daban tawa daban - Jaruma Nikki

- Fitacciyar jarumar 'yar kasar Ghana, Nikki Samonas ta bayyana abinda ba ta kauna a rayuwarta

- A hira da tayi da gidan talabijin na UTV, jarumar ta bayyana cewa babu ita babu talaka

- Ta ce baza ta iya yin soyayya da talaka ba ballantana ma ta aure shi, ta kara da cewa hanyar talaka daban ta ta daban

- Haka kuma jarumar ta ce idan akwai kudi ko yaya yake a wajen ma'aurata rayuwar su tafi tafiya yadda ya kamata

A wata hira da aka yi da ita, Nikki Samonas ta bayyana cewa baza ta taba yin soyayya da talaka ba ballantana ma kuma har ta aure shi, ta ce babu ita babu talaka a rayuwarta.

A hirar da tayi da gidan talabijin na UTV, fitacciyar jarumar 'yar kasar Ghana wacce tauraruwar ta ke haskawa a wannan lokacin, ta bayyana cewa ita ba a haifeta domin ta zo ta dinga gogayya da talakawa ba.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Kasar Saudiyya ta gayyaci manyan jaruman fim na duniya ta karramasu

Ta bayyana cewa kudi shine komai a rayuwa, kuma yana sanya abubuwa su tafi kamar yadda ya kamata a rayuwar aure idan akwai su.

Haka kuma Nikki Samonas ta bayyana cewa ta na matukar kaunar mashahurin mawakin nan na kasar Ghana wato Shatta Wale, sai dai kuma ba ta bayyana ko suna soyayya ba a wannan lokacin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng