Wata sabuwa: Kasar Saudiyya ta gayyaci manyan jaruman fim na duniya ta karramasu

Wata sabuwa: Kasar Saudiyya ta gayyaci manyan jaruman fim na duniya ta karramasu

- A kokarin da kasar ta Saudiyya take yi na ganin ta canja kasar ta koma ta zamani

- Kasar ta gayyaci manyan jaruman fim na duniya ta karrama su a birnin Riyadh ranar Litinin dinnan da ta gabata

- A cikin jaruman da aka gayyata akwai Shahrukh Khan, Jackie Chan, Jason Momoa, Jean Claude Van Damme da dai sauran su

Fitattun jarumai na duniya goma sha biyar ne suka karbi kyaututtuka a ranar Litinin dinnan da ta gabata 14 ga watan Oktobar nan, a wajen taron bikin da aka yi na karrama manyan jaruman duniya a birnin Riyadh na kasar Saudiyya, wadanda suka hada da Jackie Chan, Jason Momoa Shahrukh Khan da dai sauran su.

Fitaccen jarumin nan na kasar Saudiyya Shahrukh Khan ya wallafa sakon godiyarsa ga kasar ta Saudiyya a shafinsa na Twitter tare da sanya hotunan yadda bikin ya gudana.

A lokacin da ya zo jawabin godiya yayin da aka karramashi, jarumin ya fara ne da: 'Bismillah al-rahman al-rahim' ma'ana 'Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.'

Jarumin Shahrukh Khan Musulmi ne, amma baya nuna bambanci ga sauran addinai don matarsa mabiya addinin Hindu ce kuma sun shafe kusan shekara 28 suna tare.

Jarumin ya bayyana irin cigaban da kasar ta Saudiyya za ta samu nan bada dadewa ba duba da yadda ta bude gidajen kallo na sinima, bayan yarin kasar mai jiran gado ya cire haramcin dokar a kasar.

KU KARANTA: Ke duniya: An kama wani saurayi da kan wata kyakkyawar budurwa a cikin leda

A cikin jaruman da aka karrama akwai wata fitacciyar jaruma ta kasa masar mai suna Ragaa El Gedawy.

Haka kuma jarumin nan na fim din 'Game of Thrones' Jason Momoa ya bayyana cewa ya fada cikin kaunar kasar Saudiyya tun a karon farko da yaje kasar a shekarar 2017.

Haka shima fitaccen jarumin nan dan kasar Belgium wanda yayi suna a shekarun da suka gabata wato Jean Claude Van Damme ya ce yaji dadi kwarai da gaske da aka ba shi lambar yabo mai siffar mikiya mai ruwan gwal.

Haka zalika shi kuma jarumi Jackie Chan yana hawa mumbarin wajen taron farawa yayi da cewa: "Salam Alaikum", sannan ya cigaba da cewa "na san da yawa daga cikin ku sun sanni, na shafe shekara 59 ina yin fim, amma wannan shine karo na farko da na zo kasar Saudiyya, gaskiya Saudiyya babbar kasa ce, ina fatan sake dawowa nan gaba kadan domin daukar fim."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng