Wata sabuwa: Buhari zai kara sabon haraji a kan nau’o’in lemun kwalba da ake sha a Najeriya

Wata sabuwa: Buhari zai kara sabon haraji a kan nau’o’in lemun kwalba da ake sha a Najeriya

Ministar kudi, Zainab Shamsuna Ahmad ta bayyana cewa gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari tana duba yiwuwar tsawalla haraji akan lemun kwalba kamarsu Coke, Bigi da sai sauransu.

Jaridar The Cables ta ruwaito ministan ta bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru a taron bankin duniya da kuma bankin lamuni na duniya na shekara shekara dake gudana a kasar Switzerland.

KU KARANTA: Da dama daga cikin yan Najeriya basu iya wakar taken Najeriya ba – Minista Lai

Wannan haraji shi ke kira da suna ‘Excise Duty’, kuma ana sanya shi ne a kan kayayyakin da ake samarwa a cikin kasa, a yanzu haka Najeriya ta daura irin wannan haraji a kan duk wasu lemukan kwalba, giya, da kuma lemukan da ake yi da kayan marmari.

“Manufarmu itace mu tabbatar muna tatsan dukkanin harajin daya kamata, tare da fadada harajin da muke karba domin mu tabbatar da mun kara adadin kudaden shiga da muke samu, hakan tasa muka kara harajin VAT, da kuma duba yiwuwar kara harajin lemun kwalba, sai dai akwai hanyoyin da ake bi don cimma hakan.

“Duk wani sabon haraji da aka kirkiro sai ya bi doguwar hanya da ta kunshi tattaunawa da masu ruwa da tsaki da dama da kuma gudanar da gyaran fuska a kan wasu dokoki ko kuma samar da sabbin dokoki, haka zalika mun dauki matakan rage kudaden da ake kashewa a gwamnati.” Inji ta.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ministar tana cewa bai dace yadda Najeriya ke samar da kudaden da take aiwatar da kasafin kudinta daga man fetir kadai ba, a cewarta kasashen duniya na amfani da haraji ne waken aiwatar da kasafin kudadensu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel