Wata sabuwa: Rahama Sadau ta sake jawo kace-nace akan wani hoto da tayi tana sumbatar mace 'yar uwarta

Wata sabuwa: Rahama Sadau ta sake jawo kace-nace akan wani hoto da tayi tana sumbatar mace 'yar uwarta

- Jaruma Rahama Sadau ta sake shiga sabon cece-kuce akan sumbatar wata mace 'yar uwarta

- Sai dai wasu mutane na ganin cewa da gangan 'yan fim suke yin abubuwa na jan magana domin kada a manta da su

- Jarumar ta wallafa hoton ne a shafinta na Instagram inda sanya hoton keda wuya mutane suka yo caa kanta

Jaruma Rahama Sadau tayi kaurin suna a masana'antar Kannywood wajen sanya maudu'in da za ayi ta kace-nace a kai, zamu iya cewa tun farkon bayyanar ta ya zuwa yanzu jarumar ba ta shafe watanni uku ba tare da tayi wani abu da zai jawo magana a kafafen sadarwa ba.

Koda yake wasu na ganin da gangan 'yan fim da mashahuran mutane kanyi abubuwa na jan magana don kar a mance da su, domin wasu sunyi ittifaki da zarar an daina jin duriyar ka tofa kasuwar ka ta mutu kenan don haka sun gwammace ayi ta batun su koda na Allah wadai ne dan dai sunansu da fuskokinsu su cigaba da karakaina a kafafen sadarwa da mujallu.

KU KARANTA: Sadiya Haruna butulu ce kuma 'yar hau shiyasa bazan taba goya mata baya ba - Teema Makamashi

A yau wannan jaruma dai wani hoto ta wallafa a shafin ta inda aka ganta tana sumbatar wata mace 'yar uwarta inda wallafa hotunan keda wuya akayi caa a kanta da korafi inda har wasu shafuka suka fara wallafa hoton suna fashin baki a kai.

Koda yake mu baza mu kalli wannan ta fuskar da akasarin mutane ke kallon abun ba in muka yi la'akari da cewa a 'yan kwanakin nan mafi yawancin hotunan jarumar da mata 'yan uwanta tana kusantar su sosai fiye da kima wanda zamu iya danganta hakan da karatu da tayi a kasar waje wanda hakan ba komai bane a gurin turawa masu jajayen kunnuwa, amma a nan gida hakan ya zama abin magana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng