Sadiya Haruna butulu ce kuma 'yar hau shiyasa bazan taba goya mata baya ba - Teema Makamashi

Sadiya Haruna butulu ce kuma 'yar hau shiyasa bazan taba goya mata baya ba - Teema Makamashi

- Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood Teema Makamashi ta bayyana a bakin kotun da ake shari'ar Sadiya Haruna da Isa A. Isa

- Jarumar ta bayyana cewa ita kawai kallo ta zo, kuma babu abida za ta iya taimakawa Sadiya Haruna da shi

- Ta ce da ace ba su samu sabani ba da za ta tsaya mata har sai inda karfinta ya kare, amma banda yanzu

To dama dai shine yasa kullum ake kokarin nusantar da jama'a cewa rigima bata da dadi domin kuwa idan an san ta inda aka fara ba fa a san ta ina za ta kare ba.

Yanzu haka dai an dauki makonni ana ta faman kace-nace akan rikicin dake tsakanin jaruman Kannywood Sadiya Haruna da kuma Isa A. Isa, wacce har ya zuwa yanzu dai taki cinyewa.

A yau ne muka ci karo da wani sabon bidiyo da aka yiwa fitacciyar jarumar nan Teema Makamashi, wanda yake da alaka da wannan rikici dake tsakanin jaruman.

Kamar kullum dai dama can kowa ya san babu kyakkyawar alaka tsakanin ita Sadiya Haruna da kuma Teema Makamashi, domin kuwa kwanakin baya har tura 'yan sanda tayi suka kama ta.

KU KARANTA: Tirkashi: Budurwa ta auri kanta bayan iyayenta sun takura ta da maganar aure

A wannan bidiyon dai an nuno Teema Makamashi cikin mota inda wani mutumi wanda muke da yakinin cewa dan jarida ne yake magana da ita, jarumar ta bayyana cewa da ace ba su samu sabani da Sadiya Haruna ba da za ta tsaya mata har inda karfinta ya kare, amma yanzu ita babu ruwanta a cikin wannan rigimar taje ta karata.

Alamu sun nuna cewa jarumar ta je kotun da ake shari'ar ita Sadiya Haruna da Isa A. Isa inda har take tabbatarwa da mutane cewa tabbas anje an kamata kuma tana cikin kotu ana gabatar da shari'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng