Tirkashi: Budurwa ta auri kanta bayan iyayenta sun takura ta da maganar aure

Tirkashi: Budurwa ta auri kanta bayan iyayenta sun takura ta da maganar aure

- Wata budurwa 'yar kasar Uganda mai shekara 32 ta auri kanta da kanta

- Hakan ya biyo bayan takura ta da danginta suka yi akan sai ta fito da mijin aure

- Wannan lamari dai ya faru ne a lokacin da take bikin ranar haihuwar ta a Kampala babban birnin kasar

Wata budurwa 'yar shekara 32 mai suna Lulu Jemimah ta bar mutane cikin rudani da mamaki, bayan ta auri kanta da kanta saboda irin takura ta da danginta suka dinga yi akan tayi aure.

A yadda rahoto ya bayyana, Lulu wacce take daliba ce a jami'ar Oxford ta kasar Birtaniya, ta dauki aure a matsayin abinda za ta yi na karshe a rayuwarta bayan kammala karatun digirinta na biyu. Wannan dalilin ne ya sanya ta yanke hukuncin aurar kanta.

A lokacin da ta je Uganda bikin ranar haihuwarta a watan Agusta, Lulu ta so tayi dan kwarya-kwaryar biki na ranar haihuwarta, amma sai kawayenta suka canja mata ra'ayi inda kawai aka ganta ta yo shigar amare.

KU KARANTA: Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Yusuf ya kashe matar shi da duka saboda kawai ta kaiwa mahaifiyarta ziyara

Wannan abu ya bawa kowa mamaki, domin kuwa na ga amarya ita kadai babu ango, wanda ba kasafai mutane suka saba ganin irin hakan ba.

Lulu ta bayyana cewa ta kashe naira dari tara da hamsin ne kacal, shima kudin mota ne da ta biya aka daukota daga gida zuwa wajen bikin, sannan sauran abubuwan da ta sanya ta same su ne daga wajen kawayenta.

Duk da dai cewa iyayenta ba su samu damar halartar auren nata ba, amma sun shiga rudani akan hukuncin da ta yanke na aurar kanta da kanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel