An cafke wasu manyan masu garkuwa da mutane su 8 da ake nema ruwa a jallo

An cafke wasu manyan masu garkuwa da mutane su 8 da ake nema ruwa a jallo

Kwamishinan yan sandan jihar Imo, Rabiu Ladodo ya bayyana cewa an kama wasu gawurtattun masu garkuwa da mutane su takwas cikin 15 da ake nema ruwa a jallo a jihar.

Ladodo wanda ya bayyana haka a lokacin da ya yi wata ganawa da gwamnan jihar, Emeka Ihedioha a Owerri, babban birnin Jihar ya bayyana sunayen wasu daga cikin wadanda aka kama a matsayin; Ebike Nwadiuko, Henry Iwunze, aka Aboki, Chima Okorie, Collins Iwunze, Bernard Okechukwu da Nike wanda aka fi sani da South.

Ya cigaba da cewa daya daga cikin yan ta'addan, Nwadiuko na cikin jerin sunayen da rundunar yan sandan jihar ta wallafa tana nema ruwa a jallo.

Ladodo ya yabi Gwamna Emeka Ihedioha akan jajircewarsa wajen tabbatar da isasshen tsaro a jihar, inda ya karfafa cewa kafa ‘Operation Iron Gate’ da gwamnan ya yi na haifar da yaya masu idanu.

Ya kara da cewa tare da hadin kai da kuma goyon bayan da rundunar ke samu daga gwamnan da kuma gwamnatin jihar, tayi nasara wajen cafke masu laifi da dama da kuma rage yawan laifuffuka a jihar.

KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta mika godiya ga mijinta akan nada mata sabbin hadimai

Haka zalika, a wani lamari mai kama da haka, Ihedioha ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samu nasarori a bangaren magance kalubalen da jihar ke fuskanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel