Sabani da gwamna: Kwamishinan kudi ya ajiye mukaminsa a jihar Bauchi

Sabani da gwamna: Kwamishinan kudi ya ajiye mukaminsa a jihar Bauchi

Kwamishinan kudi a jihar Bauchi, Nura Manu-Soro, ya sanar da yin murabus daga mukaminsa bisa zargin samun sabani da gwamnan jihar a kan kudaden da gwamnati ke warewa domin dalilan tsaro (security vote).

A ranar 6 ga watan Oktoba ne gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya rantsar da sabbin kwamishinoni 20 da sauran 'yan majalisarsa inda ya bawa Manu-Soro rikon ma'aikatar kudi.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa Manu-Soro ya sanar da yin murabus dinsa a shafinsa na dandalin sada zumunta 'Facebook' a ranar Laraba.

"Na ajiye mukamina na kwamishinan kudi a gwamnatin jihar Bauchi. Zan fitar da jawabi ga manema labarai nan bada dadewa ba InshaAllah," kamar yadda Manu-Soro ya rubuta.

Duk da Manu-Soro ya goge rubutun da ya yi a shafinsa na 'Facebook' kuma bai amsa kiran da jaridar Daily Nigerian ta yi masa ba, jaridar ta bayyana cewa ajiye mukamin nasa ba zai rasa nasaba da samun sabani da gwamna Mohammed ba a kan kudin da ake ware wa domin dalilan tsaro.

DUBA WANNAN: Bauchi: Bala Mohammed ya yi wa wasu kwamishinonin gwamnatinsa garambawul

"Kun san gwamnonin kan kashe makudan kudade daga asusun jihohinsu da sunan tsaro. Shi kuma Nura da gwamna sun kasa fahimtar juna, saboda ba ya amincewa da bukatar gwamna a kan fitar da kudin.

"Ya yanke shawarar yin murabus ne bayan gwamna ya canja masa ma'aikata, canjin ma'aikatar ya bata masa rai.

"Nura na daga cikin mutanen da suka taka muhimmiyar rawa yayin yakin neman zaben Kaura, ya kashe makudan kudi wajen yi masa kamfen," a cewar wata majiya da ke da masaniya a kan abubuwan da ke faruwa, kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel