Da duminsa: Bala Mohammed ya yi 'tankade da rairaya' a gwamnatin jihar Bauchi

Da duminsa: Bala Mohammed ya yi 'tankade da rairaya' a gwamnatin jihar Bauchi

- Bala Mohammed, gwamnan jihar Bauchi, ya yi wasu kwamishinoni da ya nada garambawul

- An mayar da Nura Manu Soro zuwa ma'aikatar matasa da motsa jiki daga ma'aikatar kudi yayin da aka mayar da Umar Adamu ma'aikatar kudi daga ma'aikatar albarkatun ruwa

- Usman Muhammad, kwamishinan ma'aikatar matasa da wasanni, ya koma ma'aikatar kanana da matsaikatan masana'antu

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, ya yi garambawul ga wasu masu rike da mukaman siyasa a gwamnatin jihar Bauchi.

Kwamishin yada labarai da sadar wa na jihar Bauchi, Dakta Ladan Salihu, ne ya sanar da hakan ga manema a Bauchi ranar Laraba. Ya bayyana cewa canje-canjen da aka yi sun fara aiki nan take, ba tare da bata lokaci ba.

Ya ce an mayar da Nura Manu Soro zuwa ma'aikatar matasa da motsa jiki daga ma'aikatar kudi yayin da aka mayar da Umar Adamu ma'aikatar kudi daga ma'aikatar albarkatun ruwa.

DUBA WANNAN: Ta leko ta koma: Kotun daukaka kara ta warware hukuncin bawa APC kujerar majalisa a jihar Bauchi

Kwamishin ma'aikatar cigaban jama'a, Barista Jadauna Tula, zai koma ma'aikatar albarkatun ruwa.

Kazalika, Usman Muhammad, kwamishinan ma'aikatar matasa da wasanni, ya koma ma'aikatar kanana da matsaikatan masana'antu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel