Majalisa: Kabiru Gaya ya yi magana a kan yaran da aka rika sacewa Kano

Majalisa: Kabiru Gaya ya yi magana a kan yaran da aka rika sacewa Kano

Mun samu labari cewa Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya tashi a zauren majalisar dattawa inda ya tofa albarkacin bakinsa a game da yaran da aka sace a Kano, har aka rika sauya masu addini.

Arch. Kabiru Gaya ya yi wannan magana ne a lokacin da ya mike a gaban majalisar dattawan a Ranar Talata, 15 ga Oktoba, 2019. Wannan ya sa a karshe aka kafa kwamiti domin duba lamarin.

Kamar yadda Sanatan ya bayyana da kansa a shafinsa na Tuwita, ya kawo hujjojin wannan mummunan abu da ya faru a Garin Kano kamar yadda kafafen yada labaran kasar su ka rahoto.

Babban ‘dan majalisar ya gabatar da takardarsa inda ya nemi hukumar NAPTIP mai yaki da satar jama’a a Najeriya ta tashi tsaye wajen bankado sace kananan yara da ‘yan matan da ake yi a Kano.

KU KARANTA: An fasa zaman NLC da TUC da ‘Yan Majalisar Tarayya - Wudil

Sanatan na Kano ta Kudu ya koka da wannan mummunan ta’adi inda ya nuna tausayinsa ga halin da aka jefa Iyaye da ‘yanuwan wadannan kananan yara da aka sace, aka tsere da su zuwa Kudu.

Tsohon gwamnan na Kano ya tabo batun wata karamar Yarinya da ba ta gaza shekaru 2 ba, mai suna Aisha wanda aka tsere da ita zuwa Kudancin kasar, inda aka rikidar da ita zuwa Chioma.

Sanatan na APC ya fadawa majalisar cewa abin da yake so shi ne kwamitin harkar ‘yan sanda ta yi bincike a kan wannan sha’ani, sannan kuma ya yabawa kokarin gwamnonin Kano da Anambra.

Kabiru Ibrahikm Gaya yake cewa jihohin na Anambra da kuma Kano sun yi kokari wajen ba jami’an tsaro hadin-kai na ganin an kama wadanda ake zargi da aikata wannan mummunan laifi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel