Duk jarumar fim da Daraktoci ba sa nemanta da lalata to ta binciki kanta, akwai matsala a tare da ita - Jaruma Vicky

Duk jarumar fim da Daraktoci ba sa nemanta da lalata to ta binciki kanta, akwai matsala a tare da ita - Jaruma Vicky

- Fitacciyar jaruma 'yar kasar Ghana ta yi wata magana dangane da halin da jarumai mata ke ciki a harkar fim

- Ta bayyana cewa tabbas gaskiya ne kafin a fara sanya budurwa a fim sai an gama lalata da ita kafin a fara sanyata a fim

- Ta ce duk jarumar da darakta baya neman ta da zina to ta binciki kanta tabbas akwai matsala tare da ita

Fitacciyar jarumar nan 'yar kasar Ghana, Vicky Zugah wacce aka yi ta kace nace a kanta a 'yan kwanakin nan akan kokarin kwacewa wata mata miji, ta yi bayani akan irin cin zarafin da daraktoci ke yiwa jarumai mata kafin su sanya su a fim.

A wata hira da tayi a wani gidan rediyo mai suna Joy FM, Vicky Zugah ta ce idan har kina mace jaruma, kuma darakta ko furodusa bai taba neman yayi zina dake ba to akwai babbar matsala, ya kamat kuma ki binciki kanki.

KU KARANTA: Ba neman suna na fito yi ba a harkar fim ko yanzu na samu miji aure zanyi - Zee Pretty

Ga abinda ta ce:

"Neman lalata da jaruma kafin a sanyata a fim gaskiya ne, ba zanyi muku karya ba, yana faruwa a yanzu, kuma haka abin zai cigaba da faruwa, har ma ya zame mana jiki.

"Idan ke budurwa ce kuma kina harkar fim amma babu wani darakta ko furodusa da ya taba neman yayi zina dake to tabbas akwai babbar matsala a tare dake wacce ya kamata kije ki zauna ki nemi mafita."

Ana dai ta zargin cewa dama duk macen da take harkar fim, sai jarumai, daraktoci, furodusoshi da sauransu sun gama lalata da su kafin a sanya su a fim. Hakan ne ma ya sanya mutane da yawa suke yiwa jaruman kallon 'yan iska wadanda ake yin zina da su, har ma wadansu ke ganin baza su iya hada alaka ta aure da su ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel