Ba neman suna na fito yi ba a harkar fim ko yanzu na samu miji aure zanyi - Zee Pretty

Ba neman suna na fito yi ba a harkar fim ko yanzu na samu miji aure zanyi - Zee Pretty

- Fitacciyar jarumar nan wacce tauraruwar ta ke haskawa a wannan lokacin wato Zee Pretty ta yi wata nasiha ga 'yan fim da kuma 'yammata

- Jarumar mai suna Zulaihat Ibrahim ta yi kira ga 'yan fim da su dinga sanya tsoron Allah a harkokin su

- Sannan jarumar ta bayyana cewa ita a shirye take idan ta samu miji tayi aure a wannan lokacin

A yanzu dai za a iya cewa babu wata jaruma a cikin sabbin jarumai da ta kai Zulaihat Ibrahim wacce aka fi sani da Zee Pretty suna da kuma tashe, ba don komai ba sai don 'yan gajerun fina-finan da take yi na barkwanci tana sanyawa a shafukanta na sada zumunta.

Baya ga haka a yanzu tana da kusanci da fitaccen jarumi Adam A Zango, don haka ne ake yi mata kallon jarumar da take tashe a wannan lokacin.

Wannan yasa wakilin jaridar dimokaradiyya yayi mata tambaya akan kowanne shiri ta yiwa rayuwar ta nan gaba musamman idan ta duba yanayin 'yan fim da suka yi tashe kafin zuwanta, wadanda a yanzu wasu sun bar harkar, wasu kuma suna cikin ta amma ko tuna su ba ayi?

Sai ta ce: "To abu na farko dai shi ne tsare mutunci da kuma nuna tsoron Allah, a duk inda ka samu kan ka shine babban tanadin da ya kamata dan fim ya yiwa kansa.

"Kuma ni a yadda na dauki harkar fim na zo ne don na isar da sako domin mutane su fahimta kuma su gyara.

KU KARANTA: Tirkashi: An kama wani fasto da ya yiwa mambobin cocin shi sama da 20 cikin shege

"Kada mace ta shigo harkar fim da tunanin tana so ta yi suna don ko ba ka nemi ka yi sunan ba idan lokacin ya zo zaka yi sunan, don haka mace ta yi abin da ya dace ba wai ta zubar wa kanta da mutunci ba, don haka tsare mutunci da sanin ya kamata shi ne zai sa ki samu matsayin da kike nema.

Ta cigaba da cewa: "Duk da ina cikin harkar fim a yanzu ba wai na shiga da niyyar babu aure a gaba na ba, duk lokacin da Allah ya kawo wanda muka fahimci juna da shi sai kawai mu yi aure da shi, domin shi aure sunna ne kuma da iyayen mu ba su yi ba da ba a same mu ba, don haka suma babban burinsu shine suga munyi aure."

Daga karshe ta yi kira ga mata 'yan fim da cewar mu rinka kula da wadanda suke zuwa wajen mu da sunan za su aure mu, domin akwai 'yan yaudara sosai, don haka mata a nutsu a rinka kula da samari sosai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel