Saraki da Iyalinsa sun gaisa da Tinubu da Osinbajo a bikin Shagaya
Hotunan tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki tare da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da Bola Tinubu a wajen wani biki su na ta yawo a gari.
A cikin karshen makon da ya gabata ne aka yi wata haduwa ta musamman tsakanin Dr. Abubakar Bukola Saraki da kuma daya daga cikin jigan jam’iyyar APC a Najeriya Asiwaju Bola Tinubu.
Kusan wannan ne karon farko da aka ga Saraki tare da kusar jam’iyyar APC mai mulkin tun barinsa ofis. Saraki da PDP sun sha kasa ne a hannun APC a jihar Kwara inda ya dade ya na iko.
Manyan ‘yan siyasar sun hadu ne domin taya Attajiran Najeriyar nan watau Hajiya Bola Shagaya murnar cika shekaru 60 a Duniya. Sauran kusoshin jam’iyyar APC mai mulki sun halarci bikin.
KU KARANTA: Madugun Kwankwasiyya ya zauna da Jagoran APC a wajen walima
Rahotanni na zuwa mana cewa a lokacin da Bukola Saraki ya shiga dakin taron, ko ina ya dauki kiran ‘Oloye’. Wannan ne lakabin siyasar da ake yi wa tsohon shugaban majalisar dattawan kasar.
Daga cikin wadanda Sanata Saraki ya samu a wajen taron akwai fitaccen tsohon gwamnan jihar Legas watau Bola Ahmed Tinubu wanda ya na cikin masu karfi a siyasar Najeriya a marrar nan.
Mai girma mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya na tare da tsohon Mai gidansa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a wajen bikin. Za a iya hangen SGF, Boss Mustafa shi ma a tsaye.
Dr. Saraki yana rike ne da hannun Uwargidarsa, Toyin Saraki, wanda ta dauki lokaci ta gaida Bola Tinubu. Dattijon yana cikin wadanda su ka yi sanadiyyar tafiya hutun siyasar Maigidanta.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng