Jami'an Kwastam sun kashe mai kai wa 'yan sumoga rahoto

Jami'an Kwastam sun kashe mai kai wa 'yan sumoga rahoto

Jami'an hukumar fasa kwauri na kasa da aka fi kira da 'Kwastam' sun kashe wani mutum da ake zargi da kai wa masu sumoga rahoto a jihar Jigawa.

Jami'an hukumar sun kashe mutumin, Tasiu Muhammad, mai shekaru 22, a Unguwar Gawo, mai nisan kilomita biyar daga garin Babura a jihar Jigawa.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Jigawa, Bala Senchi, ya tabbatar da faruwar lamarin a yayin da yake gana wa da manema labarai.

Ya ce babu hannun rundunar 'yan sanda a aikin da ya yi sanadiyar kashe Muhammad.

Mazauna yankin sun ce Marigayin ya dade a cikin jerin sunayen mutanen da jami'an kwastam ke nema bisa zarginsa da bayar da bayanai ga masu shigo da shinkafar waje ta haramtacciyar hanya.

Wata majiya da ta nemi a boye sunanta saboda dalilan tsaro ta bayyana cewa jami'an Kwastam sun harbe mutumin a yayin da yake kokarin gudu wa a lokacin da suka zo kama shi. Majiyar ta kara da cewa babu makami a tare da mutumin yayin da yake kokarin gudu wa.

DUBA WANNAN: Daura: 'Yan sanda sun rufe wata cibiyar azabtar da mutane da aka gano mutum 300 a daure

Kakakin rundunar Kwastam na ofishin Kano da Jigawa, Dan-Baba, ya ce ba zai iya yin magana ba a lokacin da aka tuntube shi, saboda yana cikin wani taro, a cewarsa.

Karamar hukumar Babura ta hada iyaka da Jamhuriyar Nijar, kuma masu safarar shinkafa na amfani da hanyoyin cikin jeji wajen shigo da haramtattun kaya cikin Najeriya.

Ko a ranar Litinin, sai da shugaban hukumar kwastam, Hameed Ali, ya sanar da cewa sun rufe iyakar Najeriya na kasa, watau ba shiga ko fitar da wani kaya daga Najeriya.

Ya bayyana hakan ne yayin wani taro da manema labarai da ya gudanar tare da takwaransa, shugaban hukumar hana shige da fice ta kasa (NIS), Muhammad Babandede, a Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng