Ana wata ga wata: Hadiza Gabon ta sanya baki a rigimar Sadiya Haruna da Isah A Isah, bayan ta kirashi da dan luwadi
Ala kulli halin ita dai rigima da tashin hankali suna haifar da abinda za azo daga baya ana dana sani, domin kuwa idan an san ta yanda aka fara, ba a san yanda za ta kare ba
Ya zuwa yanzu dai an dauki wasu 'yan kwanaki ana cikin wannan tata burzar tsakanin jaruman Kannywood Sadiya Haruna da kuma Isa A. Isa, wacce har yanzu taki ci taki cinyewa.
A safiyar jiya Litinin ne 14 ga watan Oktobar wannan shekarar muka tashi da ganin wani babban sako wanda yake da alaka da wannan rikita-rikita ta Sadiya Haruna da Isa A Isa.
Wannan sako da muke magana a kai addu'ace kai tsaye daga bakin ita Sadiya Haruna, inda ta dora a shafinta na Instagram. take rokon Allah yayi mata hukunci idan har abinda ta fada akan Isa A Isa sharri ne, sannan ta yi rokon Allah ya bi masa kadi idan har karya tayi masa.
To amma yanzu dai Alhamdulillah, domin ga dukkan alamu wannan rigima da tonon silili sun zo karshe, domin kuwa jaruma Hadiza Gabon ta shigo cikin maganar. A jiya ne dai tashar YouTube mai suna Kundin Shahara ta bukaci manya su sanya baki a cikin wannan rigimar bayan wasu mutane sun fara fitowa suna maganganun da basu kamata a kan ita Sadiya Haruna da Isa A Isa.
KU KARANTA: Namijin duniya: Ahmed Isa mutumin da yayi sanadiyyar gano yaran da aka sace a Kano
To anan muna iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu, domin kuwa ga dukkan alamu jaruma Hadiza Gabon ta yiwa Sadiya Haruna magana, inda har anga ita Sadiya Haruna ta wallafa a shafinta na Instagram, tana tabbatar da cewa daga yanzu ta bar wannan magana, harma kuma ta kara da yiwa Hadiza Gabon din godiya. Ga dai abinda Sadiya Harunan ta wallafa a shafin nata na Instagram:
"Anty Hadiza Gabon wallahi ina matukar ganin girmanki, kalmomin da kika fada mini sunfi miliyan 100 a wajen. Sai lokacin da ka shiga matsalane zaka gane mai sonka, kuma In Sha Allah bazan sake cewa komai ba akan wannan batun, nagode sosai 'yar uwa."
Wannan kuma shine yake tabbatar da cewa wannan rigima ta kare a tsakaninsu sai dai kuma fatan Allah ya kiyaye gaba. Ameen.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng