Jaruman Kannnywood 7 masu tashen kudi

Jaruman Kannnywood 7 masu tashen kudi

A yayin da masana'antar shirya fina-finan Hausa da ake kira Kannywood ke kara bunkasa, wata jaridar Najeriya correctng.com dake kawo labaran masana'antun nishadantarwa na kasa ta wallafa sunayen jarumai 7 da ta ce sune kan gaba in dai maganar tashen kudi ake yi.

7. Sadik Sani Sadik

An haifi jarumi Sadik Sani Sadik a cikin shekarar 1981 a garin Jos. Jarumin ya shiga harkar fim din Hausa da kafar dama, saboda ya fito a matsayin jarumi a cikin fina-finai da suka yi shura irinsu; Maryam Diyana, Adamsy, Yan Uwan Juna, Hijira da sauransu.

He is presently active in both Kannywood and Nollywood. He is one of the greatest names in the historical backdrop of kannywood. He amassed riches for himself with the cash he got from the presidential battle he did in 2011. It is worthy to note that he has finished his mansion at Abuja.

6. Sani Musa Danja

An haifi jarumi Sani Danja a shekarar 1973. Ya kasance jarumi da ke taka muhimmiyar rawa a masana'antar Kannywood, saboda kasancewarsa furodusa, darekta, mawaki kuma gwanin rawa.

Yanzu haka yana fito wa a fina-finan kudancin Najeriya bayan kasancewarsa daya daga cikin jaruman masana'antar Kannywood, kuma duk da haka yana taba harkokin siyasa.

Jaridar ta ce yanzu haka jarumi Sani Danja ya kammala gina wani katafaren gida a Abuja.

5. Halima Atete

An haifi jaruma Halima Atete a shekarar 1988. Atete na daga cikin jarumai mata da ke da basira da kyau, nagartar da ta kai ta ga lashe manyan kyaututtuka da suka hada da jaruma mai tashe ta shekarar 2013, wacce aka bayar a Legas, kyautar jarumar fina-finan Afrika da aka bayar a kasar Ingila a shekarar 2016 da sauransu.

4. Nura M. Inuwa

An fitaccen mawaki, Nura M. Inuwa, a garin Kano a shekarar 1989. Bayan kasancewarsa mawaki, Nura ya kasance furodusa a masana'antar Kannywood. Ya dauki nauyin shirya fina-finai fiye da 10 da suka hada da; Aisha Humaira, Salma, Basma da sauransu.

3. Dauda Kahutu Rarara

Dauda Kahutu Rarara fitaccen mawakin jam'iyyar APC ne da aka haifa a jihar Katsina amma ya tashi a garin Kano. Shakka babu, mawakin na daga cikin masu tashen kudi a masana'antar Kannywood da da'irar masu sana'ar nishadantar wa a Najeriya.

2. Adam A Zango

An haifi Adam A. Zango, jarumin fina-finan Hausa, mawaki, gwamin rawa kuma furodusa a shekarar 1985 a jihar Kaduna. Ya fara harkokin fim a garin Kano kafin daga bisani ya sake koma wa jihar Kaduna bayan samun sabani da hukumar tace fina-finan jihar Kano.

1. Ali Nuhu

An haifi jarumi Ali Nuhu, daya daga cikin tsofin jaruman masana'antar Kannywood, a cikin shekarar 1979.

Tabbas Ali Nuhu ya kasance jarumi mafi shura a masana'antar Kanny, saboda gogewarsa da kuma dadewarsa a cikin harkar fim. Jarumin bai tsaya ga shirin fina-finan Hausa kawai ba, yana fito wa a cikin fina-finan kudancin Najeriya da ake yi cikin harshen turanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel