Gwamnan Kebbi ya bayar da gudunmawa naira miliyan 30 domin gina cocina

Gwamnan Kebbi ya bayar da gudunmawa naira miliyan 30 domin gina cocina

Rahotanni sun kawo cewa Gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Atiku Bagudu ya bayar da gudumuwar naira miliyan 30 ga al’umman kirista dake masarautar Zuru domin gina cocina.

Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) Rev. James Manga ne ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai.

Yace gudumuwar zai taimaki al’umman kirista a yankin Zuru wajen gina coci da sauran ayyuka.

Manga ya bayyana cewa wannan ne karo na farko da al’umman kirista ta samu makuden kudade daga gwamnan.

Ya ce baya ga gudumuwar naira miliyan 30, Gwamna Bagudu ya kuma ziyarci al’umman kirista a lokacin kirsimati da ya gabata don taya su murna.

Ya kara da cewa gwamnan har ila yau ya bada gudumuwar buhunan shinkafa da tufafi da sauran kayayyakin abinci zuwa ga cocina a fadin jihar a bikin kirsimati da ya gabata.

KU KARANTA KUMA: Zaben gwamnan Kogi: APC ta ambaci sunan wanda zai iya kayar da Yahaya Bello

Yayi kira ga gwamnan da ya tabbatar da cewa ya shigar da kiristoci majalisarsa, cewa a shekaru hudu da suka gabata gwamnan bai saka kirista ba a majalisar tasa.

Wannan ya kasance babbar kalubalen da kiristoci ke fuskanta a jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng