Ganduje ya zabi kwamishinoni na jihar Kano

Ganduje ya zabi kwamishinoni na jihar Kano

Daga karshe rahotanni daga jaridar Daily Trust sun tabbatar da cewa, gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, yana gab da kafa majalisar zartarwa ta jihar, yayin da ya fidda sunayen kwamishinoninsa.

A yayin da wannan shine wa'adiin gwamna Ganduje na karshe a kan karagar mulkin jihar, bayan ya lashe zaben ranar 23 ga watan Maris a sabon zango na biyu, akwai wasu tsaffin kwamishinoninsa guda bakwai da zai maimaita jagorancin jihar tare da su.

Wata majiya mai tushe a fadar gwamnatin ta shaidawa manema labarai cewa, cikin kwamishinonin da gwamna Ganduje zai sabunta wa'adinsu sun hadar da na ma'aikatar labarai; Malam Muhammad Garba, Murtala Sule Garo na ma'aikatar kananan hukumomi, kwamishinan raya karkara; Musa Iliyasu Kwankwaso da kuma na ma'aikatar lafiya; Dr. Kabir Ibrahim Getso.

Sauran sun hadar da kwamishinan ma'aikatar shari'a; Ibrahim Mukhtar, kwamishinan ma'aikatar kasuwanci, Ahmed Rabi'u da kuma na ma'aikatar kasafi da tsare-tsare; Alhaji Shehu Na'Allah.

A cewar majiyar, tuni gwamnan ya aike da sunayen zababbun kwamishinonin zuwa ga hukumomin tsaro da kuma hukumar NDLEA mai yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyi domin tabbatar da nagartarsu.

KARANTA KUMA: Taron Kasuwanci: Osinbajo ya tafi kasar Norway a ranar Litinin

Ta ce ana sa ran za'a fara tantance kwamishinonin a ranar Litinin, 14 ga watan Oktoba, kuma a karkare a ranar Laraba ta makon da muke ciki.

Sai dai a yayin da manema labarai suka tuntubi babban sakataren sadarwa na fadar gwamnatin Kano kuma mai magana da yawun gwamnan, Abba Anwar, ya ce ba ya da wata masaniya a kan rahoton.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel