Wacce aka ce Buhari zai aura ta dauka da gaske auren za a yi - Aisha Buhari ta yi shagube

Wacce aka ce Buhari zai aura ta dauka da gaske auren za a yi - Aisha Buhari ta yi shagube

A ranar Lahadi, 13 ga watan Satumba, Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta dawo gida Najeriya bayan ta shafe lokaci mai tsawo ba ta kasa.

A cewar wani jawabi da kakakinta, Suleiman Haruna, ya fitar, ya ce Aisha Buhari ta sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe 4:30 na safe.

Aisha ta ce ta yi murnar dawowa gida Najeriya bayan shafe lokaci mai tsawo tana hutawa a kasashen ketare.

Da take tattauna wa da manema labari jim kadan bayan saukar ta a Abuja, Aisha ta bayyana cewa wannan ba shine karo na farko da ta fara yin doguwar tafiya domin kasancewa da 'ya'yanta ba duk lokacin da suka samu dogon hutun makaranta.

DUBA WANNAN: Yunusa Ado: Hukumar DSS ta yi magana bayan sakin kasurgumin dan damfara a Kano

Sai dai ta kara da cewa zamanta a kasar Ingika ya kara tsayi ne saboda likitanta ya bukaci ta tsaya a duba lafiyarta bayan ta yi masa korafin cewa bata jin dadi sosai.

Dangane da jitar-jitar cewa ta yi yaji ne saboda shugaba Buhari na shirin kara aure, watau zai mata kishiya, Aisha ta ce wacce aka ce Buhari zai aura bata ce komai ba a kan labarin sai bayan da ranar da aka ce za a daura auren ta wuce, saboda ta yi zaton da gaske za a daura auren

BBC Hausa ta wallafa cewa; "a hirar, ta yi shagube ga wacce aka ce Buharin zai aura inda ta bayyana cewa ba ta musanta batun auren ba sai da ranar auren ta wuce tukuna ta musanta."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel