Matan jihar Adamawa sun nemi a haramta aurar da su a kananun shekaru

Matan jihar Adamawa sun nemi a haramta aurar da su a kananun shekaru

'Yan matan Adamawa, sun nemi matar gwamnan jihar, Hajiya Lami Fintiri, ta shige masu gaba wajen tabbatar da an shimfida sabuwar doka da za ta haramta wa iyayensu aurar da su a kananun shekaru gabanin su kai munzali.

'Yan matan sun yi kiran ne a ranar Juma'ar da ta gabata cikin wata rubutacciyar wasika da suka gabatar wa matar gwamnan bayan taron murnar tunawa da ranar yara mata ta duniya wacce majalisar dinkin duniya ta ware domin nazari kan al'amuran da suka shafi yara matan.

Da ta ke karanta wasikar a madadin 'yan matan cikin fadar gwamnatin jihar da ke birnin Yola, Ms Fatima Isma'il, ta ce neman a shimfida wannan doka na da muhimmanci gaske wajen bai wa yara mata damar neman ilimi tamkar sa'o'insu maza.

A rahoton da jaridar The Nation ta wallafa, 'yan matan sun kuma yi kira na neman a kara yawan malamai mata da kuma bukatar a ware makewayi daban-daban a tsakanin jinsi a makarantun jihar.

Hakazalika wasikarsu ta yi kira na neman a basu ingataccen tsaro da kariya daga afka wa tarkon fyade da saura miyagun ababe na cin zarafi da keta haddin yara a jihar.

Da take mayar da martani a kan wasikar, Uwargidan gwamna Fintiri wadda sakatariyar dindindin ta ma'aikatar harkokin mata da raya al'umma, Mrs Justina Patrick ta wakilta, ta bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta kara mayar da hankali a kan harkokin ilimi musamman na yara mata.

KARANTA KUMA: Barcelona ta fidda sunayen 'yan kwallo 4 da ka iya maye gurbin Suarez

Idan ba'a manta ba ranar 11 ga watan Oktoba ta kowace shekara, rana ce da majalisar duniya ta kebance a karo na farko a shekarar 2012 da ake nuna goyon baya ga bai wa 'yaya mata damar samun ilimi da kuma kara fadakar da al'umma irin rashin daidaiton da suke fuskanta a ko'ina a duniya.

Haka kuma majalisar ta ware ranar ne domin yin waiwaye kan halin da yara mata ke ciki musamman game da aurar da su ake yi gabanin su kai munzali.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel