Barcelona ta fidda sunayen 'yan kwallo 4 da ka iya maye gurbin Suarez

Barcelona ta fidda sunayen 'yan kwallo 4 da ka iya maye gurbin Suarez

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, ta cimma matsayar karshe dangane da wasu 'yan wasa hudu da ka iya maye gurbin dan wasanta na gaba, Luis Suarez, nan da 'yan watanni kadan yayin da tauraruwarsa ta ke ci gaba disashewa.

Babu shakka Luis Suarez wanda ya kasance dan kasar Uruguay, tauraruwarsa ta yi haske mai kafin gaske a Barcelona inda ya zuwa yanzu ya jefa mata kwallaye kusan 200 a koma tun bayan barin kungiyar kwallon kafa ta Liverpool a shekarar 2014.

Bayan shafe tsawon shekaru biyar a kungiyar, a yanzu Barcelona ta tsunduma cikin shirin lalubo wasu 'yan wasan da za su maye gurbinsa da gaggawa yayin da shekarun girma suka cimma masa.

Kafar watsa labaran wasanni ta Duniya, Fox Sport, ta ce Barcelona ta zayyana sunayen wasu 'yan kwallon kafa hudu masu jini a jiki da za su maye gurbin dan wasan nata mai shekaru 32.

Jerin 'yan kwallon hudu da kungiyar Barcelona ke shirin fita neman cefanensu sun hadar da; Lautaro Martinez na Inter Milan, Rafael Leao na AC Milan, Victor Osimhen na kungiyar Lille da kuma dan wasan gaba na kungiyar PSV Eindhoven, Donyel Malen.

KARANTA KUMA: Yadda wasu Jaruman Kannywood suka yi auren mutu'a

Dan wasan da ya fi kowa zura kwallo a kungiyar Barcelona, Lionel Messi, ya ce ya so ya barin kungiyar a 2013, amma yanzu ya yanke hukuncin cewar a kungiyar zai yi ritaya daga taka leda.

Kyaftin din Barcelona ya ce ''yana kyaunar kungiyar, kuma iyalansa suna jin dadin zama a Spaniya, saboda haka zai ci gaba da zamansa.''

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel