Innalillahi: An ceto yaran Hausawa Musulmai 'yan Kano guda 9 da aka sace aka kai su Kudu aka canja musu suna aka mayar da su Kiristoci

Innalillahi: An ceto yaran Hausawa Musulmai 'yan Kano guda 9 da aka sace aka kai su Kudu aka canja musu suna aka mayar da su Kiristoci

- Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta samu nasarar ceto wasu yara guda tara da ake sacewa ana tafiya da su jihar Anambra ana sayarwa

- Matsalar ba wai a iya nan ta tsaya ba, bayan an sayar da su ana canjawa yaran suna sannan a canja musu addini daga Musulunci zuwa Kiristanci

- An samu nasarar kwato yaran inda a cikinsu hadda masu shekaru 4, wasu da yawa daga cikinsu ma sun manta ainahin sunan su na gaskiya

Cikin wata sanarwa da aka bayyanawa maneman labarai a jiya Juma'a 11 ga watan Oktoba, mai dauke da sa hannun kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano CP. Ahmed Iliyas, ta hannun kakakin rundunar DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa, ta bayyana irin yadda rundunar ta samu gagarumar nasara wajen yaki da masa satar mutane don neman kudin fansa.

Sanarwar ta bayyana cewa a ranar 12 ga watan Satumbar da ya gabata ‘yan sanda sun samu nasarar cafke wadansu mutane da suka hada da wani mutumi mai suna Paule Owne, da kuma wata mai suna Mercy Paul Alias, masu shekaru 38, mazaunan unguwar Dakata wadanda ake zargi da satar mutane.

An cafke wadanda ake zargin ne a yayin da suke kokarin tafiya da daya daga cikin yaran da suka sace mai suna Haruna Sagir Bako zuwa garin Onitsha dake jihar Anambra.

Sun sace yaron ne a ranar 11 ga watan Satumba a lokacin da yake kan hanyar sa ta dawowa daga makarantar Islamiyya a unguwar ‘Yankaba.

Tun da farko dai mahaifin yaran mai suna Sagir Muhammad Bako ne ya sanar da hukumar ‘yan sanda cewa bai ga ‘ya’yan sa ba, masu shekaru 2 zuwa 6.

Rundunar ‘yan sanda ta musamman mai taken Operation Puff-Adder da hadin gwiwar sashen dake yaki da masu satar mutane don neman kudin fansa, ta bi diddigi kan mutanen da ake zargin.

Inda bincike ya gano cewa wadanda ake zargi sun jima suna satar mutane a unguwannin Sauna, Kwanar Jaba, Kawo, Hotoro, ‘Yankaba da kuma unguwar Dakata.

KU KARANTA: Gwaggon biri ya addabi mutanen wani kauye a kasar Afrika ta Kudu yayin da yake bin 'yan luwadi yana yi musu fyade

Binciken bai tsaya nan ba ya fadada har zuwa jihar Anambra, domin kuwa a ranar 13 zuwa 17 ga watan Satumba, ‘yan sanda sunyi nasarar tseratar da sauran yaran da aka sace daga Kano a can jihar ta Anambra, bayan da barayin suka siyar dasu, yaran da abin ya shafa sun hada da:

1. Umar Faruq Ibrahim mai shekara 10 wanda aka canja masa suna zuwa Onyedika Ogbodo

2. Aisha Mohd Abdullahi mai shekara 9 wacce aka canja wa suna zuwa Onzioma Ogbodo

3. Usman Mohammed mai shekara 5 shi ba a samu damar canja masa suna ba

4. Amira Auwal 'yar shekara 4

5. Husna Salisu mai shakara4

6. Blessing Ogbodo mai shekaru 10 ta kasa bayyana ainahin sunanta

7. Chiazozie Ogbodo mai shekaru 11 ta kasa bayyana ainahin sunanta

8. Chiemerie Ogbodo ta kasa bayyana ainahin sunanta da shekarunta

Karin mutanen da ‘yansanda suka cafke kan satar da kuma sayar da yaran sun hada da:

Emmanuel Igwe mai shekaru 34 wanda ya taimakawa masu satar mutanen sai kuma Ebere Ogbodo da wata mata louisa Daru masu shekaru 45 sune dillalan da suka siya suka kuma siyar da yaran. Sai wata mata Monica Orachaa mai shekaru 50 da suke siyarwa da yaran idan sun sato.

A karshe dai hukumar ta shawarci iyaye da su cigaba da sanya ido akan 'ya'yansu, sannan kuma suyi gaggawar sanar da hukuma idan wani abu da basu gane da shi ba ya faru da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel