Hotuna: 'Yar shekara biyar ta zama gwamnan rikon kwarya ta minti biyu a jihar Zamfara
- Wata yarinya a jihar Zamfara ta shiga tarihin gwamnonin jihar yayin da ta zama gwamnan rikon kwarya ta minti biyu kacal
- Gwamnan ya bata wannan dama ne saboda irin kokarin da take da shi a fannin ilimin zamani da kuma na addini
- Yarinyar ta sanya hannu akan wasu manyan dokoki na jihar da suka hada da fannin tsaro da kuma cigaban jihar ta Zamfara
Wata yarinya 'yar shekara biyar a duniya ta zama gwamnar jihar Zamfara ta rikon kwarya ta tsawon minti biyu.
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle ya mika ragamar mulkin jihar Zamfaran na tsawon mintuna biyu ga wata karamar yarinya 'yar asalin karamar hukumar Tsafe dake jihar ta Zamfara.
Yarinyar mai suna Asma'u Habibu Tsafe 'yar makarantar firamare ce ta Ali Akilu Model School dake garin na Tsafe.
Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya bayar da ragamar mulkin jihar na tsawon mintuna biyu ga yarinyar ne saboda kwazon ta a fannin ilimin boko da na addini.
KU KARANTA: Sojoji sun ceto daliban sakandare da aka yi garkuwa da su a Kaduna
Gwamnan rikon kwaryar ta rattaba hannu tare da zartar da wasu manyan ayyuka a jihar da suka shafi fannin tsaro da ci gaban jihar ta Zamfara.
An dai hasko hotunan yarinyar a lokacin da take zaune akan kujerar gwamnan jihar ta Zamfara rike da abin rubutu ga tulin takardu nan a gabanta, yayin da a gefe daya kuma aka nuno taron mutane da suka hada da 'yan fadar gwamnan jihar da kuma 'yan jarida.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng