Duka tatsuniyar gizo da koki ce: Bidiyon da ke yawo ba na kamun auren Sadiya Farouq da Buhari bane

Duka tatsuniyar gizo da koki ce: Bidiyon da ke yawo ba na kamun auren Sadiya Farouq da Buhari bane

Rahotanni sun kawo cewa an dauki wani bidiyo da ke yawo a matsayin na kamun auren Sadiya Umar Farouq, ministar harkoki agaji da kula da annoba, ne a ranar 14 ga wata Satumba lokaci da yan uwa da abokan arziki suka shirya liyafar nadinta.

An nada Sadiya a matsayin shugabar sabuwar ma’aikatar a ranar 21 ga watan Agusta.

Harma ta wallafa batun taron a ranar 15 ga watan Satumba, a bisa ga binciken gaskiyya da jaridar TheCable ta gudanar.

“A jiya, na halarci walimah da yan uwana da abokan arziki suka shirya domin taya ni murnar mukamin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bani a matsayin minista,” kama yadda ta wallafa.

Akwai rade-radin da ake ta yayatawa game da Ministar inda ake zargin za su yi aure da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Juma’a, 11 ga watan Oktoba.

KU KARANTA KUMA: Babu auren da shugaba Buhari zai yi a yau – Femi Adesina

Amma dai a yanzu haka tana birnin New York inda take bunkasa wani kamfen din majalisar dinkin duniya akan talauci.

A wani jawabi shafin Tuwita, ministar wacce ake rade-radin cewa itace sabuwar amaryar daurin auren da za'a gudanar a ya Juma'a, ta saki jawabin kira ga yan Najeriya kan yadda za'a kawar da talauci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel