Ba nine na takura ta ba, ita ce da kanta ta bani lambarta sannan ta fara tura mini hotunan tsiraicin ta - Malamin Jami'a ya bayyana yadda lamarin yake
- Wani malamin jami'a dan kasar Ghana ya bayyana yadda wata daliba 'yar Najeriya ta saka hotonta tsirara da kuma lambar wayar ta a cikin takardar jarabawar ta
- Malamin ya bayyana cewa idan bera yana da sata to daddawa ma na da wari, ya ce suma daliban halin su daya dana malaman
- Ya ce akwai dalibar da ya taba haduwa da ita 'yar Najeriya da take so ta kammala karatun ta ba tare da ta yi karatu ba
Malamin jami'a dan kasar Ghana, Emmanuel Acheampong ya bayyana yadda wata dalibar jami'a 'yar Najeriya ta bashi lambar wayarta daga nan kuma ta fara turo masa hotunan ta tsirara.
Da yake hira da gidan rediyon Ahotor FM, babban malamin jami'ar kasuwanci ta kasar Ghana 'Ghana Institute of Management and Public Administration (GIMPA)' ya bayyana yadda dalibai suke neman ya kwanta da su idan har zai ba su makin jarrabawa.
Idan ba a manta ba a wannan makon ne BBC ta saki wani sabon bidiyo wanda yake nuni da yadda wata ma'aikaciyar BBC tayi badda kama taje neman gurbin zama a wajen wani malami.
Bidiyon ya nuna irin halin da dalibai mata ke ciki a jami'a, inda kuru-kuru malami zai nemi ya kwanta da daliba domin ya bata maki, sannan kuma an kama wani malami a kasar Ghana yana irin wannan halayya.
KU KARANTA: An yiwa wani dalibin jami'a korar kare saboda ya nuna adawarsa ga gwamnan Taraba a Facebook
Da yake mayar da martani akan wannan abu, Acheampong ya bayyana cewa ya taba samun wata daliba 'yar Najeriya da ta ke so ta kammala karatun ta ba tare da ta yi karatu ba.
"Lokacin dana bude takardar jarabawarta babu komai a ciki sai hoton ta tsirara da kuma lambar wayarta. Na kira ta nayi mata wa'azi akan abinda take yi," in ji malamin.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng