Daukar aiki: Hukumar sojin ruwa ta saki sunayen wadanda suka yi nasara, ta yi karin bayani

Daukar aiki: Hukumar sojin ruwa ta saki sunayen wadanda suka yi nasara, ta yi karin bayani

Rundunar sojin ruwan Najerriya ta saki jerin sunayen wadanda suka yi nasara a gwajin dibar ma'aikata da ta gudanar a Lagas a tsakanin 29 ga watan Yuli da 27 ga watan Agusta.

Daraktan labarai na hukumar sojin ruwan, Commodore Suleman Dahun, ya sanar da hakan a wani jawabi a ranar Alhamis, 10 ga watan Oktoba a Abuja, inda ya kara da cewa za a iya bude jein sunayen a yanar gizo ta adireshin www.joinnigeriannavy.com.

Dahun yace wadanda suka yi nasaran zasu tafi shirin horarwa a rukuni biyu a makarantar horar da sojin ruwa wato Nigerian Navy Basic Training School (NNBTS) Onne, Port Harcourt, jihar Rivers.

Ya kara da cewa NNBTS rukunin 29A zasu fara a ranar 18 ga watan oktoba sannan NNBTS 29B zasu tafi sansanin horarwa a ranar 8 ga watan Mayu, 2020.

Ya bukaci wadanda suka yi nasara da su tafi sansanin horarwa da gajerun wando kalar shudiya guda biyu, fararen riguna biyu, farin takalmin canvas guda daya, da kuma takalmin canvas kalar ruwan kasa guda daya.

KU KARANTA KUMA: Makonni 5 kafin zaben gwamna: Gwamnan PDP ya nada sabbin hadimai guda 60

Ya lissafo sauran kayayyakin da za su kawo a matsayin, bakaken wanduna guda biyu, riguna masu dogayen hannu guda biyu, bakin taye guda biyu, bakin takalmi guda daya da kuma dogayen safa farare guda uku.

Ya yi gargadin cewa duk wanda ya iso wajen kwanaki hudu bayan ranar da aka bayyana toh ba za a bari ya shiga harabarar wajen horarwar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng