Allah daya gari ban-ban: Kabilar da samari ke kama 'yammata su yi musu dukan tsiya kafin a basu ita su aura

Allah daya gari ban-ban: Kabilar da samari ke kama 'yammata su yi musu dukan tsiya kafin a basu ita su aura

- Wata kabila a yankin kasar Habasha ta na da matukar al'ada mai abin mamaki

- Domin kuwa mace da kanta take zuwa ta roki saurayi ya zo ya zane ta a bainar jama'a sannan sai a daura musu aure

- Wannan al'ada ta zame musu abin alfahari musamman ma a wajen mata da sune suke shan wannan bakar wahala

Kabilar Hamar kabila ce dake kasar Habasha wacce aka fi sani da suna Ethiopia a turance. Wannan kabila dai ta na da wata al'ada mai abin mamaki, inda 'yammata ke rokon samarinsu su dauki bulala su zane su kafin a bari su yi aure tare.

Matan wannan kabila suna matukar alfahari da wannan duka da mazan ke yi musu, inda a al'adarsu wannan tabon na dukan yana nufin cewa dolene mijinki ya dauki nauyin rayuwarki.

Kafin a daura wa namiji aure a kabilar dole sai ya mallaki shanaye guda goma sha biyar, a wajen bikin auren ne matan da za a aura zasu fito suna rawa su kuma mazan za su dauki bulala suyi ta zabga musu a cikin jama'a.

KU KARANTA: Da duminsa: Yanzun nan wata tsohuwar Minista ta kashe kanta

Sai dai kuma akwai wani hali da matan ke ciki na abin tausayi, yayin da miji na iya dukan matarsa a duk lokacin da ya ga dama ba tare da wani dalili ba. Haka kuma matan sukan nuna tabon dukan da mazajen su suka yi musu a matsayin abin alfahari. Sannan kuma wani abin mamaki shine wannan tabon dukan shine yake nuni da kyawun budurwa a can, shine yasa ba sa rufe tabon.

Haka kuma namiji na da ikon auren mace sama da guda daya, amma kuma fa idan aka auro amarya ce za ta yi duk wata wahala ta gidan, uwargida ta na zaune tana kallon ta.

Sannan a kabilar ta Hamar dolene mace taje tayi noma, sannan ta kula da yara da sauran ayyukan gida na yau da kullum.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel