Buhari ya gana da ministocinsa a lokacin mulkin soja daga 1984 zuwa 1985
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya karbi bakuncin tsofin ministocinsa da suka yi aiki tare da shi a lokacin da ya mulki Najeriya a mulkin soji daga watan Janairu na shekarar 1984 zuwa watan Agusta na shekarar 1985.
A hotunan ganawar da hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na Tuwita, an ga shugaba Buhari da tsofin ministocin cikin farin ciki da annashuwa.
Wannan shine karo na farko da tsofin ministocin suka ziyarci shugaba Buhari a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja tun bayan zamansa zababben shugaban kasa a shekarar 2015.
Shugaban tawagar tsofin ministocin, Farfesa Ibrahim Gambari, wanda ya taba rike mukamin ministan harkokin waje, ya ce sun ziyarci shugaba Buhari ne domin taya shi murna a kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu a bangaren tsaro, yaki da cin hanci, harkokin kasashen ketare, ilimi da sauransu.
Duk a ranar Laraba, shugaba Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da mambobin kwamitin basa shawara kan tattalin arzikin Najeriya a fadar shugaban kasa, Aso Villa, birnin tarayya Abuja, kamar yadda Legit.ng ta wallafa.
DUBA WANNAN: Nan da wata uku za a fara sayar da motocin da ake kera a Najeriya - Jelani Aliyu
Mutane a fadin tarayya sun yabawa wannan kwamiti da Buhari ya nada saboda ingancin irin mutanen da ya nada.
A ranar Litinin, 16 ga Satumba, Shugaba Muhammadu Buhari ya nada wasu mutane takwas a matsayin mambobin majalisar masu bashi shawara kan harkan tattalin arziki.
Wadanda Buhari ya nada sune:
1.Farfesa Doyin Salami – Shugaba
2. Dr. Mohammed Sagagi – mataimakin shugaba
3. Farfesa . Ode Ojowu – Mamba
4. Dr. Shehu Yahaya – Mamba
5. Dr. Iyabo Masha – Mamba
6. Farfesa Chukwuma Soludo – Mamba
7. Mr. Bismark Rewane – Mamba
8. Dr. Mohammed Adaya Salisu – Sakatare
Za su rika ganawa da juna sau daya a kowanne wata tare da ganawa da shugaban kasa sau hudu a shekara. Amma shugaban kwamitin zai iya ganawa da shugaba Buhari a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng