Ta tabbata auren jaruma Sadiya Adam ya mutu, bayan an ganta ta koma otal da zama

Ta tabbata auren jaruma Sadiya Adam ya mutu, bayan an ganta ta koma otal da zama

- Kwanakin baya ake ta yada jita-jitar cewa auren jaruma Sadiya Adamu ya mutu

- Inda ita kuma ta fito a wata hira da aka yi da ita ta karyata wannan magana har take bayyana cewa tana nan a gidan mijinta

- Yanzu dai an gano cewa jarumar tana nan a cikin wani Otel dake cikin Kano dabo ta kama dakin zama

A kwanakin baya ana ta yada jita-jita akan cewa auren jaruma Sadiya Adam ya mutu, inda ita kuma a lokacin ta fito ta karyata wannan magana, inda har take bayyana cewa a yayin da take maganar ma ta dawo daga asibiti ne wajen awo, ma'ana dai tana nan a gidan mijin ta.

Kwatsam sai muka ci karo da wani rahoto wanda jaridar dimokaradiyya ta wallafa wanda yake tabbatar da mutuwar auren jarumar gami da bayyana cewa an ganta ta tare a otel din ni'ima na tsawon wani dogon lokaci ga dai abin da jaridar ta wallafa akan wannan lamari:

"Zaman me Sadiya Adamu take yi a otel din Ni'ima?

"Duk a cikin shirin 'yan fim da fina-finai, wanda jaridar Dimokuradiyya ke daukar nauyi. Daga wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano.

"To bayan mutuwar auren fitacciyar jaruma Sadiya Adamu yau kusan watanni takwas kenan ta tare a Otal din Ni'ima dake Kanon Dabo inda wasu ma suke cewa a cikin Otal din ta yi zaman iddar auren.

"Domin kuwa tun da auren ya mutu ta dawo ta tare a wajen ta zamar da Otal din nan ne wajen wuni kuma wajen kwana, saboda duk lokacin da tayi tafiya ta dawo to ba ta da wajen sauda sai otal din kuma ko da neman ta ake yi babu inda za a je a same ta in ba Otal din ba.

"Abin tun baya damun kawayenta har ya zo yana damun su, hakan ta sa wasu daga cikin kawayenta suka yi ta mata magana akan rashin dacewar hakan amma jarumar ko a jikin ta.

KU KARANTA: Hotuna: Tsofaffin jaruman Kannywood mata guda 15 da suka dawo harkar fim bayan mutuwar auren su

"A yanzu dai duk wani sammakon ka in kaje Otal din za ka iya cin karo da ita, haka ma duk daren da ka yi za ka iya samun ta don haka duk wasu da suke ganin sun isa da ita sun yi mata magana amma ko a jikin ta don haka suka yi watsi da ita.

"Saboda irin cigaba na mai hakar rijiya da Sadiya Adamu ta samu, a yanzu tsohon yaron ta wanda a baya kafin ta yi aure shi ne dan aikenta yanzu da shi take yin soyayya, kuma an ce ta kamu da son sa sosai har ma ba ta jin maganar kowa idan ba ta sa ba."

Idan har ta tabbata Sadiya ta tare a otal din Ni'ima ina makomar waccan hira da jarumar ta yi da Kannywoo Exclusive inda har ta tabbatar da cewa tana da auren ta? Dole akwai wani abu da ba daidai ba a wannan rahotannin guda biyu, ko dai jarumar ba ta fadawa Kannywood Exclusive gaskiya ba ko kuma ba ita ake gani a otal din Ni'ima ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel