Kaduna: An soma biyan Ma’aikatan kananan hukukomin Ikara sabon albashi

Kaduna: An soma biyan Ma’aikatan kananan hukukomin Ikara sabon albashi

Shugaban karamar hukumar Ikara a jihar Kaduna, Ibrahim Sadiq, ya shaida cewa ya fara biyan ma’aikatan karamar hukumar sabon tsarin mafi karancin albashin da aka amince a Najeriya.

Malam Ibrahim Sadiq yace majalisarsa ta fara biyan wannan albashi na N30, 000 ne daga Ranar 4 ga Watan Oktoban 2019. Jaridar Vanguard ta rahoto wannan ne a cikin farkon makon nan.

Sadiq ya yi wannan jawabi ne ta bakin Hadiminsa na yada labarai, Abdulmajid Hussain a babban birnin tarayya Abuja a Ranar Talata 8 ga Watan Oktoban 2019 kamar yadda mu ka samu rahoto.

A jawabin shugaban karamar hukumar ya bayyana ya dauki wannan mataki ne domin kara karfafawa gwamnatin Nasir El-Rufai wajen kokarin da ya ke yi na farfado da aikin gwamnati.

KU KARANTA: Irin albashin da 'Yan Majalisa su ke tashi da shi duk wata a Najeriya

Mai girma shugaban karamar hukumar yake cewa su na sa rai wannan karin albashi zai motsa ma’aikatan da ke aiki a kananan hukumomi wajen ganin sun yi aikin da zai kawo cigaba a jihar.

Shugaban karamar hukumar yake cewa: “Dole in furta cewa jan matakin da gwamna Nasir El-Rufai ya dauka na cika alkawarin da ya yi wa ma’aikatan jihar Kaduna ne ya kara tunzura ni.”

Sadiq yake cewa karin albashin da aka yi wa ma’aikata zai taimakawa Talakan da ke jihar inda ya kuma ce gwamnatinsa za ta cigaba da yin adalci da mulki na gaskiya a karamar hukumar Ikara.

Ba a nan kurum Hon. Ibrahim Sadiq ya tsaya ba, domin ya kara da alkawarin cewa zai inganta rayuwar ma’aikata. Kwanan nan ne dai Malam Nasir El-Rufai ya fara biyan sabon albashi a jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel