Labarin wasanni: An fatattaki Victor Valdes daga aikin Barcelona U-19

Labarin wasanni: An fatattaki Victor Valdes daga aikin Barcelona U-19

A cikin Watan Yulin bana ne aka nada Victor Valdes a matsayin Mai horas da ‘Yan wasan U-19 watau wadanda ke kasa da shekara 19. A cikin karshen makon jiya ne kuma aka sallamesa.

Abubuwa ba su kankamawa Victor Valdes da kyau ba inda ya buda wasan horaswansa a tarihi da jan kati bayan ya zagi Alkali. A wasan sa da Girona, Alkalin wasa ya kori Koci Valdes daga fili.

Jim kadan bayan samun jan kati da ukubar haramta wasanni biyu ne Victor Valdes ya yi kaca-kaca da wani Darektan kungiyar, Patrick Kluivert, wanda sun buga kwallo tare a shekarun baya.

Kluivert ya nemi Victor Valdes ya rika amfani da tsarin 4-3-3 na ‘yan wasa a madadin 4-4-2 da sabon shiga kocin ya saba da shi. Wannan ya jawo aka samu sabani tsakanin manyan Kulob din.

Daga cikin abin da ya kara jagwalgwala alakar Valdes da Kluivert shi ne yadda Kocin ya ke wulakanta Ilaix Moriba. Jaridun kasar waje sun ce wannan ya kara jefa Valdes cikin matsala.

KU KARANTA: Messi ya lashe kyautar Gwarzon 'Dan wasan Duniya

A dalilin wannan sabani ne aka hana Kocin amfani da Yaran U-18 a lokacin da manyan ‘yan wasanninsa su ka samu shiga shiga sahu na biyu na Tawagar kungiyar ta Barcelona na Barca B.

Tsohon ‘dan wasan na kasar Sifen ya koka da yadda aka hana sa buga wasa a filin Estadi Johan Cruyff inda ‘Yan kungiyar Barcelona B da ‘Yan matan Kulob din su ka saba buga wasanninsu.

A karshen wa’adin Kocin, kungiyar UEFA mai kula da kwallon kafa a Nahiyar Turai ta hukunta Valdes a dalilin zuwa wasa a makare. Valdes ya iso filin wasa a makara ne a wasansu da Inter.

Yanzu dai ana tunanin cewa Franc Artiga ne zai maye gurbin tsohon ‘dan wasan na Barcelona, Manchester da Middleborough a kulob din. Artiga shi ne ke horas da ‘yan wasan Juvenil B.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel