Dangote, Adichie da Davido, su na cikin mutane masu tasiri a Afrika - The African Report

Dangote, Adichie da Davido, su na cikin mutane masu tasiri a Afrika - The African Report

Mutanen Najeriya hudu ne su ka samu shiga cikin sahun mutane 10 na farko da su ke da karfin fada a ji da tasiri a fadin Nahiyar Afrika kamar yadda rahoton The Africa Report ya bayyana.

‘Yan Najeriyan da su ka shiga cikin wannan sahu na mutum 100 a kasashen Bakaken fatan sun hada da gawurtattun Attajirai da Masu mulki da ‘Yan wasa da Masu ilmi da manyan Marubuta.

Na farko a wannan jeri shi ne Mai kudin Nahiyar watau Aliko Dangote. Chimamanda Adiche ita ce ta hudu a jerin Fitaccen Mawakin nan Davido ne ya zo na bakwai a gaban Enoch Adeboye.

1. Aliko Dangote

Alhaji Aliko Dangote wanda ke da Kamfanin Dangote ne na farko cikin mutanen Najeriya a jerin. Attajirin ‘dan kasuwan da ya ba Naira Tiriliyan 3 baya shi ne ya sha har gaban shugaba Buhari.

KU KARANTA: Hukuma tace babu wanda zai san sirrin arzikin Shugaba Buhari

2. Chimamanda Adiche

Babbar Marubuciyar Duniyar nan Chimamanda Adiche ita ce ta zo ta hudu a kaf Afrika. Adiche ta lashe kyaututtuka bila-adadin a dalilin rubuce-rubucen da ta yi musamman wasu littafanta uku.

3. Davido

Mawakin Najeriya Davido Adeleke ne ya shigo na uku cikin mutanen Najeriya a wannan jeri. Davido shi ne na bakwai cikin mutane mafi tasiri yanzu a Afrika inji Mujallar The African Report.

4. Enoch Adeboye

Babban Malamin addinin Kiristan nan na cocin RCCG watau Fasto Enoch Adeboye ya samu shiga cikin mutanen da su ka fi kowa tasiri a Afrika. Shehin Malamin shi ne ya zo na takwas a Nahiyar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel