Ba ruwana da waye kai, zan kama mutum duk girmansa - Magu ya ci al washi

Ba ruwana da waye kai, zan kama mutum duk girmansa - Magu ya ci al washi

- Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar EFCC, ya ce babu ruwansa ko hukumar da yake jagoranta da harkokin siyasa

- A ganawarsa da manema labarai ranar Litinin, Magu ya ce babu abinda zai hana hukumar EFCC kama duk wanda ake zargi da cin hanci, ko wanene mutum

- Shugaban na EFCC ya ce EFCC ba ta amfani da jita-jita wajen gayyatar wadanda ake zargi da aikata laifin cin hanci, sai dai idan da akwai kwararan hujjoji

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC), Ibrahim Magu, ya nesanta kansa da hukumar da yake jagoranta daga shiga harkokin siyasa.

Da yake magana da manema labarai ranar Litinin, Mista Magu ya ce babu abinda zai hana hukumar EFCC kama duk wanda ake zargi da cin hanci, ko wanene mutum.

"Ba ruwana da ko kai waye, ko kuma daga inda ka fito. Ba maganar siyasa ba ce, a sabida haka ba babu bukatar bayyana shugaban jam'iyyar da ake bincika.

"In dai mutum ya aikata ko kuma ana zarginsa da laifin cin hanci, zan kama shi. Mun samu nasara a kotu a kan gwamnonin jam'iyyar APC biyu, babu tantama a kan hakan," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Tsirarun mutane da ke zaune a jihohi 5 sun tattare arzikin Najeriya - Buhari

Ya bayyana cewa hukumar EFCC ba ta amfani da jita-jita wajen gayyatar wadanda ake zargi da aikata laifin cin hanci, sai dai idan da akwai kwararan hujjojin da ke alakanta mutum da cin hanci.

"Ko an shigar da korafin mutumin da ake zargi da cin hanci sai mun gudanar da bincike mai zurfi a kansa kafin mu fara tuhumarsa, shi yasa muke gayyatar mutane, saboda akwai bukatar su bamu jawabi a kan abinda suka sani dangane da zargin da ake yi musu," a cewar Magu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel