INEC za ta dauki ma'aikata 16,139 na wucin gadi kan zaben gwamnan jihar Kogi

INEC za ta dauki ma'aikata 16,139 na wucin gadi kan zaben gwamnan jihar Kogi

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC, ta ce za ta dauki ma'aikatan wucin-gadi 16,139, saboda zaben gwamnan jihar Kogi da za a gudanar a ranar 16 ga watan Nuwamba.

Mr Festus Okoye, kakakin hukumar INEC na kasa, shi ne ya labarta hakan a ranar Talata yayin wani shirin sanin makamar aiki da horaswa da aka gudanar a kwalejin gwamnatin tarayya da ke garin Okene.

Ya ce hukumar na bukatar wannan adadi na ma'aikata domin zaben gwamnan jihar Kogi da za a gudanar a rumfunan zabe 2,548 cikin unguwanni 239 na jihar.

Ya kuma sanar da cewa, a yayin da ake daf da kammala duk wani shiri, nan da mako biyu dukkanin kayayyakin zabe za su kasance a jihar.

Ana iya tuna cewa, kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Benuwe da ke zamanta a birnin Makurdi, a ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba, ta tabbatar da nasarar gwamna Samuel Ortom kamar yadda rahotanni na jaridar The Nation suka ruwaito.

Tun a baya an ruwaito cewa, kotun za ta yanke hukunci kan shari'ar da ke tsakanin gwamna Ortom na jam'iyyar PDP da kuma abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC, Emmanuel Jime.

KARANTA KUMA: Kada ma'aikatar gwamnatin tarayya da ta sake daukar aiki ba tare da na lamunce ba - Buhari

Mista Jime wanda ya yi takarar gwamnan jihar ya kalubalanci sakamakon zaben da aka gudanar watanni kadan da suka gabata bayan da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ta tabbatar da nasarar gwamnan mai ci na PDP.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, Jime ya kalubalanci nasarar gwamna Ortoma da cewa zaben da ya gudana bai tsarkaka daga magudi ba da kuma saba wa ka'idodi na shari'a da kundin tsarin mulki ya yi tanadi

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel