Sunayen zababbun kwamishinoni 17 sun isa gaban majalisar dokokin jihar Neja

Sunayen zababbun kwamishinoni 17 sun isa gaban majalisar dokokin jihar Neja

Tsaffin kwamishinoni 9 na cikin jerin wadanda za su sake dawo wa a majalisar zartarwa ta gwamnatin jihar Neja, a yayin da gwamna Abubakar Sani Bello, ya gabatar da sunayen kwamishinoni 17 a gaban majalisar dokokin jihar domin tantancewa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, wannan rahoto na kunshe ne cikin wata rubutacciyar wasika da sa hannun gwamnan mai dauke da kwanan watan ranar 24 ga watan Satumba, wadda aka karance ta yayin zaman majalisar jihar na ranar Talata, 8 ga watan Oktoba.

Jerin kwamishinonin jihar da za su dawo a wa'adin gwamna Sani Bello na biyu sun hadar da; Barrister Nasara Dan-Mallam, Zakari Abubakar, Haliru Zakari Jikantoro, Hajiya Ramatu Mohammed Yar’Adua, Engineer Ibrahim Panti, Dr. Mustapha Jubril, Sunday Kolo, Alhaji Haruna Dukku da kuma Honorabul Mamman Musa.

Sauran da za su kasance sabbin shiga cikin majalisar zartarwa ta gwamnatin jihar sun hadar har da sakataren dindindin na ma'aikatar lafiya ta jihar, Dr. Makusidi Muhammad, Barrister Mukhtar Nasale, Alhaji Yusuf Jibril, Mr. Emmanuel Umar, Mohammed Sani Idris, Barrister Mohammed Tanko Zakari da kuma Barrister Abdulmalik Sarkin Dani.

KARANTA KUMA: Gwamna Badaru ya nada wa Matansa hadimai na musamman a Jigawa

Kakakin majalisar jihar, Honarabul Abdullahi Bawa Wuse, ya ce majalisar za tayi nazari a kan sunayen da zababbun kwamishinonin da gwamna Bello ya gabatar yayin zamanta na gaba, a yayin da daga bisani kuma za ta sanar da ranar tantance su.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel