Matashin ‘Dan wasan kwallon kafa Ezequiel Esperson ya bar Duniya a shekara 23

Matashin ‘Dan wasan kwallon kafa Ezequiel Esperson ya bar Duniya a shekara 23

Mun samu labari daga jaridun kasashen waje cewa ‘dan wasa Ezequiel Esperon ya rasu bayan ya gamu da wani mummunan hari. Wannan abin takaicin ya faru ne a cikin kasar Argentina.

Rahotanni sun zo mana Ranar 7 ga Oktoba cewa ‘dan wasan ya rasu ne sa’ilin da ya fado daga kan hawa na shida na wani dogon bene a lokacin da yake tsakiyar cashewa da Abokansa a wani gida.

Ana shekawa da Esperon mai shekara 23 zuwa wani babban asibiti mai suna Zubizarreta a babban birnin Buenos Aires na Argentina, Likitoci su ka tabbatar da cewa ya daina numfashi.

Hadarin ya auku ne da kusan karfe 3:00 na dare inda Marigayi Ezequiel Esperon da Aminansa su ke biki cikin tsakar dare a wata Unguwa mai suna Villa Devoto da ke kusa da babban birni.

KU KARANTA: Wani tsohon Kyaftin din Super Eagles ya bar Duniya

Marigayi Esperon ya fara buga kwallo ne a matsayin babban ‘dan wasa a kungiyar Buenos Aires club All Boys kafin ya koma Kungiyar nan ta Internacional da ke cikin Garin Porto Alegre.

Esperon ya buga wasansa na karshe a Duniya ne da kungiyarsa ta Atlante inda su ka sha kashi 1-0 a hannun Club Tijuana. ‘Dan wasan ya samu kati a wasannin karshen da ya buga a Mexico.

Kafin mutuwar Matashin ya zo bai da kulob din da yake bugawa. ‘Yan sanda sun tabbatar da cewa za su binciki sanadiyyar yadda ‘dan kwallon ya yi wannan hadari da ya kai ga rashin rayuwarsa.

Ana tunanin Tauraron ‘dan wasan ya jingina ne jikin bangon dogon wannan bene ta wani bangare da bai kafu da kyau ba inda ya yi wa wurin nauyi har ta kai ya fado kasa ya ce ga garin ku nan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel