Gwamna Badaru ya nada wa Matansa hadimai na musamman a Jigawa

Gwamna Badaru ya nada wa Matansa hadimai na musamman a Jigawa

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya nada hadimai na musamman ga kowane daya daga cikin matansa uku. Cikin hadimai na musamman 51 da gwamnan ya nada, akwai kuma wadanda aka ware domin kula da yawan al'umma da kuma fitilun kan hanya.

A wata sanarwar da ta fito dafa fadar gwamnatin kamar yadda jaridar Dailuy Trust ta ruwaito, an nada Sa'adatu Bashir Muhammad, a matsayin hadima ta musamman ga uwargidan gwamnan, yayin da Mariya Muhammad Mukhtar ta kasance hadima ga matarsa ta biyu da kuma Aisha Garba a matsayin hadima ga matarsa cikon ta uku wato amarya.

Haka kuma gwamna Badaru ya nada Hassan Usman Bulama a matsayin hadimi na musamman mai kula da fitilun kan hanya da kuma Surajo Musa Gwiwa, a matsayin hadimi na musamman kan kula da yawan al'umma a jihar.

A ranar Litinin da ta gabata ne kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Benuwe da ke zamanta a birnin Makurdi, ta tabbatar da nasarar gwamna Samuel Ortom kamar yadda rahotanni na jaridar The Nation suka ruwaito.

Tun a baya an ruwaito cewa, kotun za ta yanke hukunci kan shari'ar da ke tsakanin gwamna Ortom na jam'iyyar PDP da kuma abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC, Emmanuel Jime.

KARANTA KUMA: Hukumar NYSC ta tsawaita hidamar masu bautar kasa 52 a Kano

Mista Jime wanda ya yi takarar gwamnan jihar ya kalubalanci sakamakon zaben da aka gudanar watanni kadan da suka gabata bayan da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ta tabbatar da nasarar gwamnan mai ci na PDP.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, Jime ya kalubalanci nasarar gwamna Ortoma da cewa zaben da ya gudana bai tsarkaka daga magudi ba da kuma saba wa ka'idodi na shari'a da kundin tsarin mulki ya yi tanadi.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel