Kasar Saudiyya ta bawa mace da namiji 'yancin kama dakin Otal daya koda basu yi aure ba

Kasar Saudiyya ta bawa mace da namiji 'yancin kama dakin Otal daya koda basu yi aure ba

A ranar Lahadi ne kasar Saudiyya ta sanar da cewa daga yanzu bakin haure da ba jinsinsu daya ba zasu iya kama dakin Otal daya koda kuwa ba ma'aurata bane.

Wannan shine karo na farko da kasar Saudiyya ta bayar da irin wannan dama kuma ta yi hakan ne domin bawa baki masu yawon bude ido damar ziyartar kasar domin yawon bude ido ko shakata wa.

A sanarwar da hukumar kula da harkokin bude ido ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce mata 'yan asalin kasar Saudiyya kan iya kama daki a Otal matukar sun gabatar da shaidar tantance wa (ID Card) kowacce iri ce.

A baya sai miji da mata sun tabbatar da cewa su ma'aurata ne kafin su iya kama daki a Otal a kasar Saudiyya. "Yanzu babu bukatar hakan ga masu yawon bude ido," a cewar jawabin.

A ranar 27 ga watan Satumba ne kasar Saudiyya ta sanar da cewa zata bude kofofin shigowa kasar ga masu yawon bude ido ko son ziyartar kasar domin shakata wa.

Mahukuntan kasar sun yanke shawarar yin hakan ne domin fadada hanyoyin kudin shigo wa da zimmar bunkasa tattalin arzikin kasar.

DUBA WANNAN: Kotu za ta fara sauraron karar da aka shigar da Buhari a kan Osinbajo ranar Litinin

A baya kasar Saudiyya na bayar da takardar amincewa shiga kasar ne ga mata da miji da suke Musilmai kadai yayin aikin Hajji ko kuma ma'ikata bakin haure ko kuma don dalilin wasannin motsa jiki ko na al'ada.

Bude kofofin kasar domin bakin haure masu yawon bude ido ko shakata wa, na daga cikin manufofin yariman kasar, Mohammed bin Salman, na kawo gagarumin canji ga tattalin arzikin Saudiyya zuwa shekarar 2030.

Yanzu haka kasar Saudiyya ta bawa jama'a daga kasashe 49 damar neman iznin shiga kasar ta yanar gizo ko kuma a basu takardar shaidar shiga kasar da xarar sun sauka a cikinta. Yawancin kasashen da zasu ci moriyar wannan sabon tsari, kasashen Turawa ne.

Sai dai, kasar ta ce zata ci tarar duk wadanda suka yi shigar da ke nuna tsiraici ko kuma suka nuna soyayya a bainar jama'a ko a wuraren da basu dace ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel