Jihar Jigawa da Neja za su fara biyan mafi karancin albashi na N30,000 a karshen watan Oktoba

Jihar Jigawa da Neja za su fara biyan mafi karancin albashi na N30,000 a karshen watan Oktoba

- A karshen watan Oktoba gwamnatin jihar Jigawa za ta fara biyan mafi karancin albashin ma'aikata na N30,000

- Gwamnatin jihar ta bayar da sahalewarta a kan fara biyan sabon mafi karancin albashin ma'aikatan ta

- Alhaji Hussaini Ali Kila, mukaddashin shugaban ma'aikatan jihar, shi ne ya sanar da hakan ga manema labarai

Gwamnatin jihar Jigawa ta bayar da sahalewar fara biyan sabon mafi karancin albashin na Naira 30,000 ga ma'aikatan jihar a karshen wannan wata na Oktoba da muke ciki a shekarar 2019.

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar a yayin ganawa da manema labarai ta sanar da hakan ne ta bakin mukaddashin shugaban ma'aikatan jihar, Alhaji Hussaini Ali Kila.

Jaridar Legit.ng ta tattaro cewa, gwamnatin jihar za ta gudanar da wani muhimmin zama tare da kungiyar kwadago reshen jihar a ranar Talata, 8 ga watan Oktoba domin tabbatar da kudirin fara biyan mafi karancin albashin ma'aikata.

KARANTA KUMA: A makon da ya gabata an kashe sojoji 38 da fararen hula 16 a Najeriya

Haka kuma a wani rahoton mai nasaba da wannan, gwamnatin jihar Neja ta amince da fara biyan mafi karancin albashin ma'aikata na naira 30,000 da zarar ta kammala tantance ma'aikatan jihar.

Wannan sanarwa na kunshe cikin wani rahoto da sa hannun Abdullbergy Ebbo, mai magana da yawun gwamnan jihar Neja, Abubakar sani Bello.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel