Tun muna yara muke wasan ango da amarya, sai gashi Allah ya hada aurenmu yanzu - Amarya ta bada tarihin rayuwarsu

Tun muna yara muke wasan ango da amarya, sai gashi Allah ya hada aurenmu yanzu - Amarya ta bada tarihin rayuwarsu

- Wata matar aure, wacce tayi aure kwanan nan ta bayyana yadda ta auri mijinta

- A cewar amaryar mai suna Brendaline, tun suna wasan yara na ango da amarya sai gashi yanzu Allah ya hada aurensu

- Amaryar ta bayyana cewa tabbas komai yin Allah ne, saboda tunda take bata taba ganin irin wannan ya faru da wasu ba

Wata amarya mai suna Brendaline, ta bayar da tarihin rayuwarsu ita da mijin da ta aura, duk da cewa iyayensu abokanan juna ne na tsawon shekaru da yawa, tun ma kafin su zo duniya.

A wani rubutu da ta wallafa, Brendaline ta bayyana cewa lamarin su ya fara tun suna wasan ango da amarya ita da mijin nata a lokacin suna yara kanana, sai gashi yanzu sun zama ango da amaryar a gaske. Ta bayyana cewa auren nasu bashi da alaka da abokantaka dake tsakanin iyayensu, saboda sun jima da rabuwa, sai Allah ya kara hada su a shafin sada zumunta.

KU KARANTA: Abin dariya a kotu, yayin da wanda ake tuhuma yabi alkali da itace zai rafke, bayan ya yanke mishi hukuncin da bai yi masa ba

"Ni da iyaye na mun bar garin da muke da zama a da, kuma mun daina magana da iyayen shi har zuwa shekarar 2013, kwatsam sai gashi mun hadu a shafin sadarwa na Facebook.

"Na tuna lokacin da Babana yake daukar mijina a hannunshi, bai san cewa zai zo ya zama sirikinsa ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel