Kullu Nafsin Za'ikatul Maut: Awanni kadan ya rage a daurawa Fatima aure sai Allah ya karbi rayuwarta

Kullu Nafsin Za'ikatul Maut: Awanni kadan ya rage a daurawa Fatima aure sai Allah ya karbi rayuwarta

- Awanni kalilan suka rage a daura auren Fatima da masoyinta Abdulbasiru, sai Allah ya karbi rayuwarta

- Mutuwar wannan baiwar Allah ta girgiza mutane da dama, domin kuwa zazzabi ne ya rufe ta daren jiya Juma'a, cikin abinda bai fi minti 40 ba Allah ya karbi ranta

- An shirya daura musu aure da angonta a yau Asabar ne a Masallacin Dahiru Bauchi dake cikin garin Kaduna

An ce ana bikin duniya ake na kiyama, hakan kuwa ta faru akan wata budurwa mai suna Fatima Abubakar Yola, inda ya rage sauran dan kankanin lokaci a daura mata aure Allah ya karbi a barsa.

Fatima dai ta rasu a cikin daren jiya Juma'a inda ake sa ran za'a daura mata aure a yau asabar dinnan da misalin karfe 1:30 na rana.

Fatima dai ta rasu ne sanadiyyar wani zazzafan zazzabi na Typhoid da ya rufe na 'yan mintuna, inda cikin minti arba'in da fara rashin lafiyar sai Allah ya karbi rayuwarta cikin daren.

KU KARANTA: Tsananin talauci ya sanya saurayi tono gawar mahaifinsa da ya mutu shekaru 14 da suka wuce, domin ya cire kayan da aka binne shi da su

Fatima Abubakar Yola dai an shirya daura mata aure da masoyinta mai suna Abdulbasiru Tijjani Saminu, wanda suka shafe shekaru suna soyayya, inda aka bayyana za ayi daurin auren a Masallacin Sheikh Dahiru Usman Bauchi dake cikin unguwar Tudun Wada a cikin birnin Kaduna.

Muna yi mata addu'ar Allah yayi mata rahama ya sanya Aljannah Firdausi ta zamo makomar ta. Shi kuma ango da wannan rashi ya faru dashi Allah ya kara masa dangana ya kuma canja masa da mafi alkhairi. Amin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel